NASWDEN Ta Yaba Wa Ministan Tsaro Badaru Kan Ƙoƙarinsa Wajen Ƙarfafa Tsaro a Najeriya 

Ƙungiyar Dillalan Tattara Shara da Takin Gida ta Najeriya (NASWDEN) ta yabawa Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, bisa gudummawarsa wajen inganta tsarin tsaro a Najeriya. 

Ƙungiyar, wacce ke wakiltar dillalan sharar gida da tarkace a faɗin ƙasar nan, ta jinjina wa ƙoƙarin Ministan wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali, musamman a yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma da ke fama da rikice-rikice. 

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, Shugaban NASWDEN na reshen Arewa maso Yamma, Kwamared Aminu Hassan Soja, ya bayyana cewa jagorancin Ministan ya kawo sauyi mai kyau. 

“Minista Badaru ya zama wani tauraro mai haske a yaƙi da rashin tsaro,” in ji Kwamared Soja. 

“Jagorancinsa ya haɗa kan rundunonin tsaro, ya ƙarfafa shiga tsakanin al’umma, kuma ya inganta hanyoyin magance ƙalubalen tsaro ba tare da amfani da ƙarfi ba. Sakamakon haka, muna ganin kyakkyawan ci gaba a harkar tsaro a jihohin da abin ya shafa.” 

NASWDEN ta kuma yaba da matakan da Ministan ya ɗauka na yaƙi da satar man fetur a yankin Niger Delta, inda ta yaba wa yadda ya lalata hanyoyin aiyukan ‘yan ta’addar. 

Ƙungiyar ta ce waɗannan matakan sun taimaka wajen bunƙasa tsaro da kuma samun tsayayyen tattalin arziƙi a yankin. 

“Mu a matsayin ƙungiya da ke aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron kayayyaki da ayyuka, muna miƙa cikakken yabo ga sadaukarwar Minista Badaru wajen kare ƙasarmu,” in ji Kwamared Soja. 

“Hanyarsa ta ɗaukar matakai masu zurfi, waɗanda suka haɗa aiki na soja da samar da haɗin kan al’umma, ta zama misali na shugabanci mai inganci a fannin tsaro a Najeriya.” 

Ƙungiyar ta yi alƙawarin ba da cikakken goyon baya ga Ministan Tsaro, Mai Ba da Shawara Kan Tsaro na Kasa, da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ƙoƙarinsu na gina Najeriya mai tsaro da wadata. 

NASWDEN ta kuma sake nanata ƙudirinta na aiki tare da gwamnati da hukumomin tsaro domin magance tushen rashin tsaro, tare da jaddada muhimmancin samun zaman lafiya mai ɗorewa ta hanyar shiga tsakanin al’umma da samar da dabarun ƙirƙire-ƙirƙire.

Badaru AbubakarNASWDEN
Comments (0)
Add Comment