NATO Na Bikin Cika Shekaru 75 Da Kafuwa

Ministocin ƙasashen waje na rundunar NATO wadda aka kafa a shekarar 1949 domin magance barazanar sojojin rusashshiyar Tarayyar Sobiyat ga kasashen Turai sun taru domin murnar cikar rundunar shekaru 75 da kafuwa.

Bikin dai ya gudana ne duk da cibayan da ake samu a rikicin da ake a Ukraine, yayin da Babban Sakataren NATO, Jens Stolttenberg ke kira ga muhimmancin haɗin kai a lokacin da ake samun saɓani.

Stoltenberg ya tunawa Amurka rawar da zata taka a cikin rundunar, inda ya jaddada buƙatar samun Amurka da Turai a tare domin samun tsaro da zaman lafiya.

Ya kuma bayyana wasu muhimman gudunmawa da ƙasashen Turai da ke rundunar ke bayarwa da suka haɗa da na ƙarfin soji, binciken sirri da kuma hulɗa da ƙasashe.

Shugabannin Turai sun bayyana damuwarsu kan makomar NATO, musamman a yanayin da ake ciki na rashin tabbas a siyasar Amurka da kuma tsaikon da ake samu wajen temakawa ƙasar Ukraine.

NATO
Comments (0)
Add Comment