NBA Dutse Ta Alƙawarta Inganta Ayyukan Lauyoyi Don Hanzarta Yanke Shari’a A Jigawa

Daga: Mika’il Tsoho, Dutse

Rashen ƙungiyar lauyoyi ta NBA a Dutse, Jigawa, ya alƙawarta inganta ƙa’idojin aiki da riƙon gaskiya tsakanin lauyoyi domin hanzarta shari’a a jihar.

Shugaban reshen, Mustapha M. Kashim, ya bayyana hakan yayin bikin Ranar Shari’a na 2025 da aka gudanar a Dutse, inda ya ce taken wannan shekara shi ne “Upholding Justice Through Ethical Advocacy” wato Tabbatar da Adalci ta Hanyar Ƙarfafa Gwiwa.

Ya ce reshen yana mayar da hankali kan horaswa da koyar da lauyoyi domin inganta tsarin shari’a da amfanin jama’a.

Gwamna Malam Umar Namadi ya yaba wa shugabannin NBA kan haɗin kai da ƙwazo wajen tabbatar da tsari da gaskiya a fannin shari’a.

“Na sha bin yadda kuka gudanar da reshen NBA a jihar nan cikin tsari da haɗin kai mai ƙarfi, wanda ke amfani ga lauyoyi da jama’a baki ɗaya,” in ji gwamna.

Ya ce taken wannan shekara na Law Week ya dace domin tunatar da lauyoyi muhimmancin aiki bisa gaskiya da inganta shari’a.

Gwamna Namadi ya bayyana wasu ayyukan gwamnati kamar kafa Cibiyoyin Shari’a na Al’umma wato Community Law Centres da Zauren Sulhu domin ƙara samun adalci a ƙasa.

Ya kuma yi kira ga duk masu ruwa da tsaki su yi aiki da gaskiya da bin tsari.

Gwamnan ya kammala da fatan cewa taron zai taimaka wajen inganta ƙa’idojin aiki da hanzarta shari’a a jihar.

Comments (0)
Add Comment