NG-CARES: Masu Cin Gajiyar Shirin Sun Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Amfani da Tallafi a Jigawa

Daga Ibrahim Ibrahim

Masu cin gajiyar shirin Nigeria COVID-19 Action Recovery and Economic Stimulus (NG-CARES) Results Area II a Jihar Jigawa sun sa hannu kan wata yarjejeniyar amfani da tallafin don tabbatar da ingantaccen amfani da kayan tallafi da aka bayar ƙarƙashin shirin. 

Yayin rabon injinan yin kwai a Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa, Shugaban FADAMA CARES na jihar, Dr. Aliyu Inuwa, ya jaddada mahimmancin yarjejeniyar wajen cimma manufofin wannan tsari. 

Dr. Inuwa ya nuna damuwa kan yadda aka sha ƙin yin amfani yanda ya dace da tallafin gwamnati a baya, yana mai cewa akwai buƙatar tabbatar da gaskiya da ɗaukar alhakin duk wani tallafi da aka bayar. 

“Wannan yarjejeniya wata alaƙa ce tsakanin gwamnati da masu cin gajiyar tallafin. Manufarta ita ce tabbatar da cewa an yi amfani da albarkatun yadda ya dace domin cimma burin farfaɗo da tattalin arziƙi da ɗorewar cigaba,” inji shi. 

Ya bayyana cewa shirin NG-CARES Results Area II ya tallafa wa sama da mutum 47,790 a Jihar Jigawa don farfaɗowa daga tasirin annobar COVID-19. 

“Mun tallafa wa mutum 47,790 da suka haɗa da: manoman shinkafa 3,360, masara 2,210, dawa 4,330, gero 3,650, da masu kiwon kaji 1,660.

“Sauran sun haɗa da: masu kiwon awaki 5,700, tumaki 1,330, injinan sarrafawa 710, injinan ruwa 4,210, kifaye 100, karnukan gida 1,280, kayan zuma 100, injinan yin taliya 550, injinan haƙa rijiya 170, injinan yin ƙwai 270, kayan abinci 16,200, da kayan kariya na mutum 270.”

Dr. Inuwa ya jaddada cewa za a sa ido sosai kan masu cin gajiyar shirin don tabbatar da bin dokokin yarjejeniyar, yana mai gargaɗin cewa duk wanda ya saɓa wa yarjejeniyar zai fuskanci hukunci. 

“Wannan shiri ba wai kawai don farfaɗowa ba ne, don samar da hanyar dogaro mai ɗorewa ne ga mutanenmu. Masu cin gajiyar tallafin dole ne su bi ƙa’idojin don ganin an cimma burin wannan tsari,” ya faɗa a ƙarshe. 

Shirin NG-CARES na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen rage tasirin annobar COVID-19 a tattalin arziƙi tare da samar da damar bunƙasar dogaro na dogon lokaci a Jihar Jigawa.

Comments (0)
Add Comment