A jihar Neja, sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar rundunar tsaro ta haɗaka da goyon bayan bayanan sirri daga hukumar DSS sun kashe aƙalla ƴan bindiga 45 a wani farmaki da suka kai a garin Iburu da ke ƙaramar hukumar Shiroro.
Rahotanni daga jami’an tsaro sun bayyana cewa DSS ta bayar da bayanan gaggawa kan jin motsin wasu mahara masu yawa da ke shirin kai hari, lamarin da ya sa sojoji suka shirya tsaf.
An yi artabu mai zafi, inda aka kashe ƴan ƙalilan daga cikin maharan kuma aka lalata babura da dama da suka zo da su.
WANI LABARIN: Wasu Gwamnonin Na Shirin Komawa APC Kuma Zargin Ƙuntatawa Ba Gaskiya Ba Ne – Gwamnan Nasarawa
Wata majiya ta ce mutanen ƙauyukan yankin sun ƙirga gawarwaki fiye da 40 a cikin daji da kewaye, tare da tabbatar da cewa wasu daga cikin bindigogin da aka ƙwato manya ne.
Duk da nasarar da aka samu, an rasa rayukan mambobi biyu na rundunar haɗakar, yayin da wasu huɗu ke karɓar magani a babban asibiti sakamakon raunin harbin da suka samu.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da addabar sassan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
Hukumomi sun bayyana cewa farmakin na daga cikin sabbin dabarun gwamnati na murƙushe ƴan ta’adda kafin su kai hari.