Nigeria Za Ta Jagoranci Ƙoƙarin Samar da Wutar Lantarki Ga Mutane Miliyan 300 A Afirka

Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa Najeriya na taka rawar gani a shirin samar da lantarki ga mutane miliyan 300 a nahiyar Afirka kafin shekara ta 2030, inda ya jinjina wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da tallafin dala biliyan ɗaya ga hukumar wutar lantarki a karkara a watan Disambar 2024.

Yayin jawabinsa a taron ƙoli na farko da aka gudanar a Legas kan makamashi mai tsafta da haɗin gwiwar hukumar Samar da Ci gaba ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP), Kakakin ya ce Najeriya ta zama jagora a wannan yunƙuri ta hanyar shirin Mission 300 tare da haɗin gwiwar Bankin Duniya da na Afirka.

“Nasarar wannan sauyi tana buƙatar haɗin gwiwa da tsare-tsaren doka daga ƴan majalisa, aiwatarwa da gaskiya daga ɓangaren zartarwa, jari daga masu zuba jari, da kuma wayar da kai daga ƙungiyoyin fararen hula,” in ji Kakakin.

WANI LABARIN: Gwamnatin Tarayya Za Ta Magance Rikicin Manoma da Makiyaya A Jigawa – Sanata Malam Madori

Ya bayyana cewa majalisar wakilai ta riga ta zartar da ƙudirin sauya haraji wanda ya cire VAT daga kayan aikin lantarki mai tsafta da fasahar iskar gas ta CNG, don ƙara ƙarfafa saka jari a fannin makamashi mai tsafta.

Kakakin ya kuma bayyana cewa majalisar na ƙoƙarin samar da kariya ta doka ga tsarin REEEP na 2015, wanda ke nufin ƙara amfani da makamashi mai tsafta da rage hayaƙi mai gurɓata iska.

Ya ce a shekarar 2024 kaɗai, kaso 92 cikin 100 na sabon karfin wutar lantarki a duniya ya fito ne daga makamashi mai tsafta, inda ya ce “wannan wata sabuwar hanya ce ta tsarin tattalin arziƙin makamashi na duniya.”

Kakakin ya bayyana cewa daga cikin tallafin dala biliyan ɗaya da shugaban ƙasa ya amince da shi, dala miliyan 750 za a yi amfani da su ne wajen samar da wutar lantarki ta hasken rana a yankunan da ba su da isasshen lantarki, wanda hakan zai amfanar da mutane fiye da dubu dari biyu a fadin Najeriya.

Comments (0)
Add Comment