Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya, NAF sun musanta tallallukan da ke zagayawa a kafafen sa da zumunta cewa suna ɗaukar sabbin ma’aikata.
Rundunar ta bayyana cewa masu yaɗa tallallukan na ƙoƙarin yaɗa ƙarerayi ne da kuma yunƙunrin damfarar masu neman aiki.
A jawabin da Daraktan Hulɗa da Jama’a na NAF, Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar a safiyar Litinin ɗin nan ya ce, “NAF ba sa ɗaukar ma’aikata,” inda ya gargaɗi masu neman aikin da kar su faɗa hannun ƴan damfara.
Gabkwet ya ce tallen bai samo asali daga rundunarsu ta NAF ba, yayin da ya tunawa ƴan Najeriya cewa, a ranar takwas ga watan Yuli ne suka yaye sabbin sojojin sama waɗanda suka yi Basic Military Training Course 43/2022.
Ya ƙara da cewa, a duk lokacin da rundunar zata ɗebi sabbin ma’aikata, za ta sanar da al’umma yanda ya kamata.
“Ana sanar da al’umma cewa, ɗaukar ma’aikata a rundunar NAF kyauta ne ba tare da an karɓi wata kyauta daga main nema ba. Duk wanda ya biya kuɗi ga wani a dalilin neman aikin to shi ya jiyo.
“Haka kuma NAF ba ta da wasu wakilai da sunan masu wucewa gaba a ɗaukar aiki, saboda haka duk wanda ya ce shi jami’i ne na hakan to ɗan damfara ne.
“Rundunar ta kuma yi kira ga masu neman aikin da su fallasa duk wanda ya nemi kuɗi a wajensu ga Rundunar NAF ko ofishin ƴansanda mafi kusa,” in ji shi.