Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama mai ƙarfi da iska daga ranar Laraba zuwa Juma’a a sassan kasar nan.
A cikin rahoton yanayi da ta fitar a jiya Talata, NiMet ta ce ana sa ran za a sami mamakon ruwan sama a jihohin Borno, Adamawa, Taraba, Yobe, Katsina, Sokoto, da Kaduna a lokutan safiya, yayin da aka yi hasashen samun ruwan da yamma a jihohin Kano, Borno, Katsina, Adamawa, Kaduna, Taraba, Zamfara, Kebbi, da Jigawa.
A yankin tsakiyar arewa, za a sami ruwan a Abuja, Nasarawa, da Neja da safe, sannan daga bisani za a sami ruwan a wasu sassan Abuja, Nasarawa, Benue, Kogi, Neja, da Kwara.
A kudancin kasar, an yi hasashen za a sami ruwan a jihohin Oyo, Osun, Ekiti, Ogun, Ondo, Legas, Edo, Delta, Cross River, da Akwa Ibom da safe, sannan daga baya a sami ruwan sama mai tsanani a wasu sassan Enugu, Ebonyi, Abia, Anambra, Edo, da wasu jihohin kudancin kasar.
NiMet ta yi gargaɗin gujewa yankunan da ke da haɗarin ambaliya saboda yawan ruwan sama mai karfi da ake sa ran zai haifar da ambaliya a manyan birane da dama.
Hukumar ta kuma shawarci jama’a da su riƙa sauraren bayanai daga NiMet domin samun labaran yanayi da kuma gudar tafiya a lokacin da ake hasashen guguwar iska da ruwan sama.
NAN