NNPP Ta Ce Kwankwaso Ba Shi Da Damar Ƙara Yin Takara A Ƙarƙashinta

Jam’iyyar NNPP ta ce tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa a 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba shi da hurumin sake amfani da jam’iyyar wajen tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 2027.

Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dr Agbo Major ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar, yana mai cewa Kwankwaso da abokinsa Buba Galadima tuni an kore su daga jam’iyyar saboda laifin cin amanar jam’iyya.

Wannan na zuwa ne bayan iƙirarin Galadima na cewa, Kwankwaso zai ci gaba da kasancewa cikin NNPP har zuwa lokacin da siyasar 2027 za ta fara zafi, inda ya ce: “Zamu tsaya mu jira har lokacin ya yi, kuma muna buƙatar goyon bayan ƴan Najeriya domin Kwankwaso ya karɓi shugabanci.”

WANI LABARIN: Batun Karɓa-Karɓa Zai Iya Zamewa ADC Alaƙaƙai, Yayin Da Atiku, Obi Da Amaechi Ke Bayyana Son Yin Takara

Sai dai Dr Agbo ya ce, “Kwankwaso ya kawo mana rikici da dama ciki har da canza tambarin jam’iyya zuwa tambarinsa na Kwankwasiyya,” yana mai ƙari da cewa “ba za mu sake yarda da shi ba.”

Ya ce Kwankwaso yana mafarkin samun tikitin jam’iyyar kamar yadda ya yi a 2023, amma wannan karo ba zai yiwu ba domin yanzu NNPP za ta bi doka da tsarin jam’iyya wajen zaɓen ɗan takara.

“Kwankwaso ba shi da ƙwarewar da za ta ba shi damar fafatawa da Shugaba Tinubu, don haka ya dakatar da burinsa tun kafin lokaci ya ƙure masa,” in ji shi.

Dr Agbo ya ƙara da cewa, duk wata magana da Kwankwaso da Galadima ke yi ba ta da nasaba da jam’iyyar NNPP, yana mai ba da shawarar cewa, su kafa sabuwar jam’iyya su yi takararsu a cinkinta amma ba NNPP ba.

Comments (0)
Add Comment