NNPP Za Ta Binciki Kwankwaso Kan Zargin Badaƙalar Sama Da Naira Miliyan Dubu Na Jam’iyya

Ɗaya daga cikin tsagin jami’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ƙarƙashin jagorancin Major Agbo, ya sanar da cewar zai binciki ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen da ya gabata, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da wasu makusantansa kan zargin yin badaƙala da sama da naira miliyan dubu da aka tara a lokacin siyar da famafaman takara ga ƴan takara.

Wannan na zuwa ne tare da zargin da tsagin na NNPP yake yi wa Buba Galadima na fifitawa tare da ƙaƙaba wasu ƴan jam’iyyar a kan wasu yayin tsayawa takara.

Waɗannan zarge-zarge sun bayyana ne a sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai na NNPP tsagin Agbo, Abdussalam Abdulrasaq ya raba bayan kammala zaman tattaunawa da suka yi a ofishin jami’iyyar na ƙasa, jiya a Abuja.

Ya ce, NNPP za ta gudanar da ƙwaƙƙwaran bincike kan badaƙalar sama da naira miliyan dubun da aka tara yayin siyar da famafaman takara ga ƴan takara daga watan Maris na shekarar 2022 har kawo wannan lokaci.

KARANTA WANNAN: PDP Ta Cika Shekaru 25 Da Kafuwa, Ta Ce Shekarunta Na Mulki Ne Gwalagwalai Ga Najeriya

Ya ƙara da cewar, jam’iyyar ta amince da shigo da jami’an tsaron da suka dace domin bincikar asusun jam’iyyar da nufin neman bayanai daga Kwankwaso, tsohon shugaban jam’iyyar da ya sauƙa a watan Maris, 2023, korarren shugaban jam’iyyar da kuma korarren sakataren jam’iyyar na ƙasa.

Abdulrasaq ya ce, za su yi hakan ne domin ƙara ƙwarin guiwa ga ƴan jam’iyya da ƴan takara da su ka sayi takardun tsayawa takara da kuɗaɗensu da suka samu daga guminsu.

Haka kuma jam’iyyar ta NNPP ta tuhumar dalilin mayar da Ɗakin Tattara Bayanan Jam’iyyar zuwa gidan Sanata Rabiu Kwankwaso na ƙashin kansa, abin da ta ce ya haifar da halin badaƙala da cin hanci da rashawa da kuma maguɗi wanda ya bai wa Buba Galadima damar yin ƙaƙaben ƴan takara.

Abdulrasaq ya kuma tabbatar dacewar, NNPP ta janye daga yarjejjeniyar da aka yi da Kwankwasiya Movement da kuma National Movement, inda ya ce mutanen waɗancan gungu biyu sun shigo ne domin kawar da asalin wanda ya kafa jam’iyyar ba kuma ta hanyar da jam’iyyar ta tsara ba na damawa da kowa.

Da yake mayar da martani, Mai Binciken Kuɗi na Ƙasa na Jam’iyyar, Ladipo Johnson ya wanke Kwankwaso daga dukkan zarge-zargen da ake yi masa, inda ya ce zuƙi ta malle ce kawai.

Ladipo ya ce ai ba Kwankwaso ne ya siyar da famafaman takara ba, sanna kuma ya yi mamakin cewar, sai yanzu shugabannin tsagin suke wannan maganar bayan an dakatar da su daga jam’iyyar.

Buba GaladimaNNPPRabiu Musa Kwankwaso
Comments (0)
Add Comment