NNPP Za Ta Fitar Da Matsaya Tsakanin Goyon Bayan Tinubu, Shiga Haɗaka Ko Ci Gaba A Haka

Gabanin zaɓen 2027, jam’iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso ta saka ranar 28 ga Agusta don taron shugabanninta, NEC mai muhimmanci domin yanke matsayar dabarunta na siyasa, a cewar mai magana da yawunta, Ladipo Johnson.

“NNPP tana bayar da dama ga mafita uku da muka sha faɗa: mu kafa ƙawance ko haɗin gwiwa, mu ci gaba a matsayin NNPP mu kaɗai mu tunkari zaɓe, ko kuma mu mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin zarcewa,” in ji shi.

Jam’iyyar za ta tattauna kan sake duba kundin tsarin mulkinta, jerin tarurrukanta na kogres da babban taron ƙasa, da nazarin sakamakon zaɓukan cike-gurbi da kuma “tsarin ƙara samun sabbin mambobi da sabuwar rajista” domin faɗaɗa ƙarfinta a fadin ƙasa, tare da jaddada cewa “siyasa tana tafiya, amma ayyukanmu su kasance cikin ƙa’idoji da ƙima; kuma maslahar ƙasa muhimmiyar abar tambaya ce.”

Johnson ya roƙi mambobi “su kwantar da hankalinsu” har sai an yanke hukunci a taron, yana mai cewa duk matakin da za a ɗauka “za a yi shi ne domin ya zama mafi alheri ga jama’a.”

A halin yanzu, jam’iyyar ta umarci mambobinta da magoya baya su yanki rijistar zaɓe ko su sabunta ta, a matsayin matakin farko na manyan shirye-shiryen zaɓen 2027.

Comments (0)
Add Comment