OPC Ta Ce Shugabannin Ƙasa Yarabawa Ba Su Nunawa Arewa Wariya Ba

Ƙungiyar Oodua People’s Congress (OPC) ta ƙaryata iƙirarin cewa Shugaba Bola Tinubu da tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo sun goyi bayan Yarbawa a kan Hausawa ko wasu ƙabilu a lokutan mulkinsu.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƙasa na OPC, Akin Adesina, ya ce Buba Galadima na NNPP ne ya yi wannan zargin a wata tattaunawa a talabijin, yana zage-zage kan zanga-zangar Ilorin ta 1999 zuwa 2000.

Adesina ya bayyana cewa “a Kwara, kimanin kashi 70 cikin 100 Yarbawa ne na asali, ba sa buƙatar ɗaukar mutanen waje su yi faɗa a madadinsu, musamman a Ilorin,” yana mai tambayar dalilin haɗa sunayen Tinubu da Obasanjo.

Ya tuna rikicin Saki a Oktoban 2000, inda “rahotannin hukumomin tsaro suka nuna Fulani makiyaya ne suka kashe manoma,” ya ƙara da cewa “rahotannin suna nan don tabbatarwa.”

Ya ce “menene ruwan Obasanjo da kare OPC, alhali shi ne ya bayar da umarni a 1999 na a harbi ƴan OPC idan sun tayar da tarzoma,” don haka zargin kariya daga shi ba shi da tushe.

Ya kuma ce “babu abin da ya haɗa Tinubu da lamarin Ilorin,” yana kira ga Galadima ya daina kalaman nuna rarrabuwar kai.

“Muna sa ran jin kalaman haɗin kai, ba zuga rikici ba,” in ji OPC, tana mai cewa marigayi Fasehun da shugaban yanzu Osibote sun san Galadima a matsayin aboki, don haka wannan iƙirarin nasa ya girgiza su.

Comments (0)
Add Comment