‘Oyoyo Baba!’ – Badaru Ya Jawo Hankalin Dubban Magoya Baya A Babura, Yayin Da Jam’iyyar APC Ta Nuna Ƙarfi

Dubban magoya baya sun taru a ranar Asabar don maraba da Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, yayin zuwansa Jihar Jigawa domin zaɓen cike-gurbi na Babura/Garki a mazaɓarsa, abin da ya sa ake ganin an wanke jita-jitar cewa zai iya gujewa zaɓukan saboda rikicin cikin gida na APC.

Tururuwar mutanen sun riƙa rera waƙoƙi, inda mutane suke cewa “Oyoyo Baba” domin nuna farin cikin su ga dawowar ministan gida, lamarin da ya bayyana ƙarfin goyon bayansa a yankin.

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin akwai rarrabuwar kai tsakanin masu goyon bayan Badaru da waɗanda ke goyon bayan Gwamna Umar Namadi, amma zuwan Badaru ya sauke damuwar tare da nuna wani sabon haɗin kai tsakaninsu.

Duk da rashin halartarsa a manyan taruka a baya ciki har da wani babban gangamin jam’iyyar a makon da ya gabata, bayyanarsa a yau ta karfafa gwiwar masu zaɓe da yawa.

Manyan jami’an jam’iyya sun ce halartar Badaru alama ce ta jajircewa wajen ganin nasarar APC da kuma ci gaban Jigawa, inda wasu suka ce hakan na iya taimakawa wajen sasanta rigimar siyasar da ke tsakani.

An ga ƴan takara da shugabanni suna zagayawa tare da ministan cikin walwala, lamarin da ya ƙara nunawa jama’a cewa jam’iyyar na kan ƙoƙarin samun haɗin kai.

Musa Shehu, ɗaya daga cikin dattawan APC, ya yi tsokacin cewa, “zuwan Minista Badaru a yau ya rushe dukkan jita-jita”, kalaman da suka ƙara ƙwarin gwiwa a tsakiyar taron jama’ar.

Comments (0)
Add Comment