A daidai lokacin da zaɓen gwamnoni na ranar 11 ga watan Nuwamba wanda za a yi a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi ke ƙara ƙuratowa, Jam’iyyar PDP ta ƙirƙiri kwamiti na musamman kan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a kan manufofin jam’iyyar da tsare-tsarenta ga al’umma.
Kafa kwamitin mai ɗauke da mutane 12, kamar yanda Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na Jam’iyyar, Debo Ologunagba ya faɗa a yau Talata, ya dace da tanadin doka a Sashi na 40 (1) (a), (b) da (c) na kundin tsarin mulkin PDP kamar yanda aka sabunta shi a 2017.
Ologunagba ya ce, aikin kwamitin shine ya haɗa guiwa da kwamitoci daban-daban da ake da su a kan zaɓuɓɓukan domin tabbatar da an samar da ingantacciyar hanyar sadarwa da wayar da kan jama’a domin samun nasarar jam’iyyar PDP.
Kwamitin wanda zai samu shugabancin shi Debo Ologunagba, yana da Richard Ihediwa a matsayin Sakatare.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Emmanuel Ibeshi, Kola Ologbondiyan, Emmanuel Ogidi, Segun Sowunmi da Richard Akanmode.
Akwai kuma Don Evarada, Alfred Kemepado, Arthur Ugochukwu, Ezekwe Uche da Ibu Thomas.
Jam’iyyar ta kuma yi kira ƴaƴan nata da su zagaya loko da saƙo a jihohi ukun, domin tabbatar da samun nasarar PDP da ƴan takarkarunta a zaɓuɓɓukan masu zuwa.