PDP Ta Buƙaci INEC Ta Sanya Lokacin Gudanar Da Zaɓen Cike Guraben Ƴan Majalissu 25 Na Jihar Rivers

Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta yi kira Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, da ta sanya ranar gudanar da sabon zaɓen cike guraben ƴan majalissun Jihar Rivers 25 da suka fice daga jam’iyyar suka koma jam’iyyar APC.

PDP ta ce buƙatarta ta dace da Sashi na 109 (1) (g) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

PDPn ta bayyana cewar babu wata mafita ga ƴan majalissu 25 ɗin da suka bar jam’iyyar suka koma jam’iyyar APC.

PDP ta ce, duba da Sashi na 109 (1) (g) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, ƴan majalissun da suka bar jam’iyyar sun bar kujerunsu saboda barin jam’iyyar da suka yi.

A sanarwar da jam’iyyar PDP ta saki a yau Talata, Mai Riƙon Shugabancin Jam’iyyar, Umar Iliya Damagum ya ce, jam’iyyarsu na jaddada cewar tun da yanzu sun bar jam’iyyar sun kuma rasa kujerunsu, zaɓi ɗaya da ya ragewa ƴan majalissun shine su sake tsayawa takara idan suna son dawowa majalissar duba da tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Damagun ya jaddada cewar babu wata ɓaraka a jam’iyyar PDP a ƙasa ko a jiha da zata halasta fitar ƴan majalissun daga jam’iyyar.

Ya ce saboda wannan dalilin ba su damar ƙara dawowa majalissar jihar har sai in sun sake shiga zaɓe sun sami a nasara kamar yanda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 da kuma Dokar Zaɓe ta 2022.

Ya ƙara da cewar, Kakin Majalissar Jihar Rivers, Barr. Ehie O. Edison ya sanar da barin gurbin ƴan majalissun 25 waɗanda suka sauya sheƙa kamar yanda Sashi na 109 (1) (g) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya nuna.

Ya ce, yana bayar da shawara ga ƴan majalissun da kar su yaudaru da duk wani abu da wani da ke Abuja zai faɗa musu na nuna musu cewar zasu iya komawa majalissar ba tare da sun ƙara tsayawa zaɓe ba, ko ya nuna musu cewar za a iya dakatar da Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, daga aiwatar da sabon zaɓe a majalissunsu.

INECPDP
Comments (0)
Add Comment