PDP Ta Cika Shekaru 25 Da Kafuwa, Ta Ce Shekarunta Na Mulki Ne Gwalagwalai Ga Najeriya

A jiya Alhamis ne, jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta cika shekaru 25 da kafuwa, inda ta bayyana shekarunta 16 na mulkin Najeriya a matsayin shekarun da suka zama gwalagwalai ga Najeriya da ƴan Najeriya.

A wani jawabi da yai Abuja kan cikar jam’iyyar shekaru 25, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na PDP, Debo Ologunagba ya ce, jam’iyyar ta yanke hukuncin yin ƙananan bukukuwa saboda babu wani abin murna a wannan lokaci saboda, a cewarsa, jam’iyyar All Progressives Congress, APC ta wargaza duk ci gaban da PDP ta kawo a tsawon shekaru 16 cikin shekaru 8 kacal.

Ya ce, PDP na murna dagewar ƴan Najeriya kan mulkin demokaraɗiyya, musamman ma waɗanda suka assasa lamarin da kuma mambobin jam’iyyarsu ta PDP, bisa sadaukarwarsu da gudunmawar da suka bayar wajen dawowar mulkin demokaraɗiyya da samun dorewarta a Najeriya.

Ya ce, yana kan gaba-gaba a tsarin PDP na cewar mulki na al’umma ne, wannan ta sa jam’iyyar yin biyayya ga tsarin dokoki, da tsarin damawa da kowa da kuma bai wa kowa ƴanci, da tabbatar da ƴancin ƴanjaridu da gudanar da ingantaccen zaɓe.

Ya ƙara da cewar, jam’iyyar PDP ta samar da bunƙasuwar tattalin arziƙi, samar da ci gaban ababen more rayuwa, ɗaukar ma’aikata da samar da damarmakin kasuwanci da sauran abubuwan alkhairi, abin da ya sanya shekarun PDP a matsayin shekarun da Najeriya ta fi samun ci gaba a tarihinta.

KARANTA WANNAN: Ƴan Najeriya Na Nadamar Cin Zaɓen Tinubu Da APC, In Ji PDP

Debo Ologunagba ya ƙara da cewar jam’iyyar PDP ta bunƙasa harkokin sa ka hannun jari daga ƴan ƙasa da kuma baƙi ƴan ƙasashen waje a dukkan fannoni har sai da ta kai kasuwanci a Najeriya na cikin mafiya samun riba a duniya.

Ya ce, amma abin baƙin ciki, dukkan nasarorin da PDP ta samarwa Najeriya, jam’iyyar APC ta durƙusar da su, abin da ya sa cikin shekaru takwas kacal, tattalin arziƙi ya lalace har ƙasar ta zama cibiyar talauci ta duniya da tarun marassa aikin yi da yawansu ya kai kaso 35 cikin 100.

Ya kuma ce, APC ta jawo tsananin yunwa ga ƴan Najeriya da ƙyale ɓullar baƙin cututtuka da haifar da yawaitar mutuwar ƴan ƙasa.

Ologunagba ya ce, a ƙarƙashin gwamnatin APC, manyan kamfanonin duniya na barin Najeriya; yayin da darajar naira tai matuƙar faɗuwa daga naira 197 a dala ɗaya zuwa sama da naira 900 a dala ɗaya; man fetur da ake siyar da shi a naira 87 duk lita kafin zuwan APC, yanzu ya koma sama da naira 600.

Ya ce baya da waɗannan ma akwai ƙare ƙaren wahala ta haraji kala-kala da tsadar biyan kuɗaɗen abubuwa da cirewa mutane kuɗaɗe waɗanda jam’iyyar ta APC ta ƙaƙabawa ƴan Najeriya.

Ya ƙara da cewar, rayuwa a Najeriya ta yi matuƙar wahala, ta yanda a yanzu ƴan Najeriya na siyar da rayuwarsu da miƙa kansu cikin bauta a ƙasashen waje domin su samu sauƙi.

Ya kuma ce, jam’iyyar APC ta yaudari mutane wajen karɓar mulki ta hanyar amfani da ƙarerayi, sannan kuma tana amfani da ƙarfi da cin zarafi da maguɗi wajen ganin ta ci gaba kasancewa a karagar mulki.

Sakataren Yaɗa Labaran na PDP, Ologunagba ya kuma ce, jam’iyyar PDP na kira ga ƴan Najeriya da kar su bari guiwarsu ta sare a kan Najeriya, inda ya ƙara da cewar, jam’iyyarsu ta PDP za ta ci gaba da kasancewa tare da su a duk inda ci gabansu ya ke.

APCPDP
Comments (0)
Add Comment