PDP Ta Sanar Da Rana Da Wajen Zaɓen Sabbin Shugabanninta

Jam’iyyar PDP ta sanya ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba, 2025 domin gudanar da babban taronta na ƙasa da zaɓen sabbin shugabanni a birnin Ibadan.

A cewar wata sanarwa daga taron NEC da aka gudanar a Abuja, an amince da jadawalin ayyuka da tsarin gudanar da taron na bana.

Jam’iyyar ta jaddada cewa “PDP jam’iyya ce mai ƙarfi, haɗin kai, da hangen nesa wajen ceto ƙasa daga mulkin APC da ake ganin ya gagara.”

WANI LABARIN: JERIN SUNAYE: Lauyoyi 57 Da Suka Samu Ɗaukaka Zuwa Matsayin SAN A Najeriya

An umurci shugaban jam’iyyar Iliya Damagum da sakataren jam’iyya Sanata Samuel Anyanwu da su sanar da INEC domin cika doka.

NEC ta kuma kafa kwamitin gudanarwa da na raba muƙamai zuwa yankuna domin tabbatar da ingantaccen zaɓe cikin gaskiya da adalci.

“NEC ta buƙaci NWC da ta ɗauki matakin shari’a kan mambobin da suka sauya sheƙa daga PDP,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar ta sake nanata aniyar ta na haɗa kai da ƴan Najeriya masu kishin ƙasa domin kawar da mulkin APC a 2027.

Comments (0)
Add Comment