RANAR MATASA: Ka Yunƙura Ka Fi Ƙarfin Masu Bautar Da Kai Ya Kai Matashi

Daga: Comrade Musa Isma’il Birnin Kudu

Ni bana murna da ranar matasa don ba mu san kanmu ba har yanzu, mun biyewa kwaɗayi, maula, tumasanci da shirmen azzaluman ƴan siyasar da rayuwarsu ta kusan ƙarewa suna juya mana tunani suna ruguza rayuwarmu ta hanyar hada mu gaba a tsakaninmu saboda banbancin jam’iyya.

Suna sace arzuƙin ƙasarmu don gina kansu da rayuwar iyalansu. Sun mallaki kuɗin da hankali ma ba zai iya kashe su ba. Sun ƙwace damarmu sun bautar damu ta hanyar ƙaƙaba mana talauci da rashin sanin makoma. Sun hanamu karatun zamani da na addini. Sun dasa mana tsoron idan na ƙi bin umarnin honorable wane gobe ba zai bani ƴar naira 5000 da ya ke ba ni ba –  wanda ko kuɗin kati da data da kake sakawa kake ɓatawa kai da ƴan uwanka bai kaiba.

Ya kai matashi wanda kake da gobe mai nisa ya kamata ka shiga taitayinka ta hanyoyi kamar haka:

Ka rabu da zaman majalisa ka kama neman ilimi na zamani da na addini.

Ka rabu da zaman gidan honorable ka kama zaman shago ko wajen sana’a don neman na kwabo da taro.

Ka rabu da mugun tunani na zan yi karatu don nai aiki a gwamnati, kafara nazarin zan yi karatu don nasamu gogewa don fadi tashin yanda zan nemi taro da sisi na samarwa wasu aikin yi.

Karabu da jayaya a social media ka kama tallata hajar ka komi kashin kasuwancinka da kake gani.

 Ka ƙara nazari ka rabu da abubuwa da yawa da suke zame maka tarnaƙi wajen samun ci gabanka da ciyar da na kusa da kai gaba. Ka cire tsoro da fargaba da kwaɗayin samu cikin sauƙi. Ka yi burin zama babba mai arziƙi da zamewa sanadiyyar arziƙin wasu, Allah zai temakeka.

Ba Haushe ya ce, ‘Allah Ya ce tashi in temake ka,’ ka motsa ka yunƙura ka fi ƙarfin masu bautar da kai ya kai ɗan’uwana matashi – ina yi maka fatan alkhairi.

Comrade Musa Isma’il Birnin Kudu

Musa Isma'il
Comments (0)
Add Comment