Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 29 ga watan Mayu a matsayin ranar hutun ma’aikata sakamakon bikin rantsar da Shugaban Kasa mai jiran-gado, Bola Ahmed Tinubu.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya ce an ba da hutun ne saboda bikin murnar demokaraɗiyya.
Rabon da a yi hutun demokaradiyya a ranar 29 ga watan Mayu a Najeriya dai tun shekarar 2018, bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da Ranar Demokaraɗiyya zuwa 12 ga watan Yuni na kowacce shekara, inda sai a ranar ne ake yin hutun.
To sai dai kuma, a bana babu tabbas ko ma’aikata zasu sake samun hutun a ranar 12 ga watan Yunin mai zuwa.
Buhari ya ce ya ɗauki matakin ne don girmamawa da kuma tunawa da Moshood Abiola, wanda ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993 amma gwamnatin soja ta soke zaɓen.
Tuni jami’an tsaro suka tsaurara tsaro a birnin Abuja kafin bikin rantsar da Bola Tinubu a ranar Litinin a matsayin shugaban Najeriya na 16.