Rashin Cin Jarabawar JAMB Alama Ce Ta Yaƙi Da Satar Jarabawa Na Nasara – Ministan Ilimi

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa yawan ɗaliban da suka kasa samun maki sama da 200 a jarrabawar UTME ta shekarar 2025 wata shaida ce da ke nuna cewa gwamnati na samun nasara a yaƙi da maguɗin jarrabawa.

JAMB ta fitar da sakamakon da ya nuna cewa daga cikin ɗalibai miliyan 1.95 da suka rubuta jarrabawar, kimanin ɗalibai 420,000 ne kawai suka samu maki fiye da 200, wanda ke nuna cewa sama da kashi 78% sun gaza samun kaso 50% na makin jarabawar.

Alausa ya bayyana a wani shirin talabijin na Channels cewa, “Wannan alama ce ta gaskiyar sakamako saboda tsauraran matakan tsaro da JAMB ta kafa a tsarin jarabawa na CBT.”

WANI LABARIN: Yau Majalissar Dattawa Za Ta Yanke Hukuncin Ƙarshe Kan Ƙudirin Gyaran Haraji Da Ke Ci Gaba Da Jawo Cece-Kuce

Ya ƙara da cewa, “Ba za mu iya cewa haka ga WAEC da NECO ba, inda ake yawan samun satar jarabawa.”

Ministan ya ce, gwamnati na ƙoƙarin fara juyar da jarabawar WAEC da NECO zuwa tsarin CBT tun daga Nuwamban 2025, inda za a fara da ɓangaren objective kafin a shigar da ɓangaren essay a shekarar 2026.

“Dole ne mu yi amfani da fasaha don yaƙar damfara,” in ji shi, yana mai cewa akwai cibiyoyin da ake kira ‘miracle centres’ da ke haifar da ɓarna ga nagartattun ɗalibai.

Ya ce, “Mafi munin abu game da maguɗi shi ne yadda yake hana ƙwazo da jajircewar masu ƙoƙari; dalibai suna shiga hanyar maguɗi idan suka ga wasu sun mallaki tambayoyi tun kafin lokacin fara jarabawa.”

Comments (0)
Add Comment