Ribadu Ya Ce Mutane 47,000 Ne Suka Mutu A Arewa Saboda Matsalar Tsaro

Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa fiye da mutane 47,000 ne suka mutu sakamakon rashin tsaro a Arewacin Najeriya kafin Bola Tinubu ya hau mulki a watan Mayun 2023.

A cewarsa, Najeriya ta kusa rugujewa lokacin da gwamnatin Tinubu ta karɓi ragamar mulki, ta sha fama da ƙalubale da dama da ke barazanar haɗin kan ƙasa da rayuwar al’umma gaba ɗaya.

Yayin da yake jawabi a wurin taron cika shekaru 50 da kammala karatu na ƙungiyar daliban makarantar soji ta NDA zubi na 18 a Abuja, Ribadu ya bayyana halin da ƙasar ta tsinci kanta a ciki a matsayin “wata gaskiya mai tayar da hankali.”

Ya ce gwamnatin Tinubu ta gaji ƙalubalai biyar masu tsanani: Boko Haram a Arewa maso Gabas, ƴan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, masu gwagwarmayar ɓallewa a Kudu maso Gabas, masu fasa bututun mai a yankin Niger Delta, da rikicin ƙabilanci a jihohi kamar Benue da Filato.

“Boko Haram kaɗai ta hallaka fiye da mutane 35,000 a Arewa maso Gabas, tare da raba miliyoyi da muhallansu,” in ji Ribadu, inda ya ƙara da cewa rikice-rikicen da ke Arewa maso Yamma da ta Tsakiya sun kashe sama da mutane 12,000, sun raba miliyan ɗaya da muhallansu, kuma sun hana yara miliyan ɗaya zuwa makaranta.

WANI LABARIN: An Kama Manajan Gidan Mai Da Wasu Mutane Bisa Zargin Aikata Fashi

Ya kuma bayyana cewa a shekarar 2022 kaɗai, an kashe mutane 1,192 kuma an sace 3,348, ciki har da hare-haren jirgin ƙasa na Kaduna, harin sojojin Guards Brigade a Abuja, da harin coci a Owo.

Ribadu ya ce gwamnatin Tinubu ta samu ci gaba mai yawa, inda aka kashe ƴan ta’adda 13,543, sama da 124,000 daga cikinsu suka miƙa wuya, an kuma ƙwato makamai 11,118 da harsasai fiye da dubu 252,000.

A cewarsa, yanzu an samu zaman lafiya a Kudu maso Gabas, an sake gina ofisoshin ƴan sanda fiye da 50, an kuma hana tasirin dokar tilasta zaman-gida da IPOB ke tilasta wa a baya.

A yankin Niger Delta kuwa, Ribadu ya ce an dawo da ƙarfin samar da ɗanyen da a yanzu ya kai ganga miliyan 1.8 a rana, kuma an rusa wuraren tace ɗanyen mai haramtattu guda 1,978 tare da ruguza wasu tukunen dafa mai 3,773.

Ya ƙara da cewa “Zamu dawo da aikin haƙo mai a ƙasar Ogoni bayan fiye da shekaru 30 ba a yi.”

A ƙarshe, ya roƙi tsofaffin sojojin NDA da su bayar da gudummawa wajen tsara tsare-tsaren tsaro na ƙasa, yana mai cewa: “Ƙwarewarku da iliminku a harkar tsaro tamkar taskar ƙasa ce da dole mu ci gaba da amfani da ita.”

Comments (0)
Add Comment