RIGIMAR SARAUTA: Malaman Musulunci Sun Roki Tinubu Da Ya Bari A Zauna Lafiya A Kano

Kungiyar Malaman Musulunci a Jihar Kano, Ulama, sun roƙi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya sanya baki tare da kare duk wani abu da zai kawo hatsaniya da karya doka a jihar.

A wata sanarwa da mambobin Ulama 18 suka sanya wa hannu, malaman sun nuna damuwarsu kan rikicin sarautar Kano da ke faruwa a halin yanzu.

Malaman sun bayyana muhimmancin da ke cikin shigar Tinubu wajen daukar duk matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Sun bayyana cewar Gwamnatin Jihar na da bukatar samun haɗin kai da goyon bayan Gwamnatin Tarayya.

Waɗanda suka sanya hannu a sanarwar sun haɗa da Shaykh Abdullahi Uwais Limanci, Shaykh Ibrahim Khalil, Shaykh Abdulwahab Abdallah, Shaykh Nasir Adam, Shaykh Aminu Ibrahim Daurawa, Shaykh Bashir Tijani Usman, Shaykh Sukraij Salgha, Khalifah Tuhami Shaykh Atiku, Dr Bashir Aliyu Umar, Khalifah Hassan, Shaykh Sani Kafinga, Shaykh Abba Adam Koki, Shaykh Ibrahim Shehu Maihula, Professor Muhammad Babangida Muhammad, Shaykh Jamil al Qadiri, Shaykh Ali Abdulkadir Abdulkadir, Dr. Abdulmutallib Ahmad Muhammad, Dr Khidir Bashir Abdulhamid da kuma Shaykh Aminu Adam.

An samu hatsaniya a Kano biyo bayan umarnin da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar na gaggauta kama tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

Jihar Kano
Comments (0)
Add Comment