Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na yankin Arewa maso Yamma, Malam Salihu Lukman, ya sanar da ajjiye muƙaminsa a shugabancin jam’iyyar.
Lukman ya miƙa takardar ajjiye aikin ne a jiya Laraba ga Shugaban Riƙo na Jam’iyyar, Sanata Abubakar Kyari.
Ajjiye aikin Lukman dai na zuwa ne, mako guda bayan Sanata Abdullahi Adamu da Iyiola Omisore sun ajjiye muƙamansu na Shugaban Jam’iyya na Ƙasa da Sakataren Jam’iyya na Ƙasa.
A takaradar ajjiye aikin da Lukman ya rubuta, ya bayyana cewa, “Rankaidade, ina sanar da kai cikin aminci cewa, na ajjiye muƙami na na Mataimakin Shugaban Jam’iyya na shiyyar Arewa maso Yamma na babbar jam’iyyarmu, All Progressives Congress. Ajjiye aikin nawa ya fara aiki nan take, abin da ya zame min dole duba da yarda ta cewa yanayin jam’iyyarmu yana cikin matuƙar saɓani da abin da aka kafa ta a kai.
Labari Mai Alaƙa: Illoli Huɗu Na Rashin Naɗa Ministoci Kan Lokaci
“Maimakon ci gaba da kasancewa a cikin shugabancin jam’iyyar da kasancewa ta tarnaƙi ga shugabanni, musamman ga jaririyar gwamnatin Shugaban Ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai fi min na sauwaƙewa kaina na huta da harkokin siyasa.”
Lukman ya bayyana cewar, yana nan a cikin jam’iyyar “da fatan shugabanninmu, musamman Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, zai guji aikata aiyukan da zasu zama rashin adalci da saɓa doka, waɗanda suke da muhimmanci ga dukkan wani iƙirari na kasancewa ɗan demokaraɗiyya ko mai son kawo ci gaba a matsayin ɗan siyasa ko mai kishin Najeriya.”
Malam Salihu Lukman ya yabawa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai bisa miƙa sunansa da kuma goyon bayansa tsawon lokacin da yai a shugabancin jam’iyyar.
Kwanaki shida da suka gabata dai, an ga Lukman lokacin da ya rubutawa Gwamnonin APC takarda yana nuna rashin jin daɗinsa kan zargin yunƙurin zaɓar tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje a matsayin wanda zai maye gurbin Abdullahi Adamu na shugabancin jam’iyyar na ƙasa.