Rikicin Cikin Gidan Da Ke APC Da PDP Ya Fi Na Labour Party – Peter Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi a jiya Laraba ya bayyana cewar jam’iyyarsu zata magance matsalolinta na cikin gida tare da samun ƙarin ƙarfi.

Peter Obi wanda yake jawabi ga manema labarai Ya bayyana cewar, rigingimun cikin gida na jam’iyyar Labour Party ba su kai irin waɗanda jam’iyyun APC da PDP ke fama da su ba.

A yanzu haka dai jam’iyyar Labour Party na fama da rikicin cikin gida wanda ya samo asali daga cire shugaban jam’iyyar Julius Abure da Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC ta yi.

Baya da wannan rikicin kuma, akwai rikicin da yake addabar jam’iyyar wanda ke da alaƙa da tsagin Lamidi Apapa wanda ke rikicin shugabancin jam’iyyar da tsagin Abure.

Peter Obi ya ƙara da cewar, ba shi da halin son canzar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin ko a mutu ko ai rai.

Peter Obi
Comments (0)
Add Comment