RIKICIN SUDAN: Rundunar RSF Ta Kai Farmaki Filin Jirgin Sama Tare Da Wani Wurin Ajiyar Makamai

Rundunar sojin ƙasar Sudan ta bayyana cewa dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun kai hari da jiragen yaƙi marasa matuƙa a wani sansanin soja da ke kusa da filin jirgin saman Port Sudan, tare da wasu wurare da suka haɗa da wajen ajiye kaya da kuma wuraren fararen hula.

A wani rahoto da Al Jazeera ta fitar daga Khartoum, wakiliyarta Hiba Morgan ta ce “a cewar shaidu daga cikin birnin Port Sudan, an harba jirage marasa matuƙa guda biyar da suka kai harin kai tsaye kan wurin sojoji,” lamarin da ke nuna shi ne karon farko da RSF ta kai hari a gabashin ƙasar.

Rundunar sojin ta bayyana cewa harin ya yi sanadin ɓarnata wani wuri da ake adana makamai, duk da cewa har yanzu babu wani rahoto da ke nuna asarar rayukan fararen hula.

WANI LABARIN: Kiraye-Kirayen Ayyana Dokar Ta Ɓaci A Zamfara Mugun Nufi Ne – Ƙungiyar Ƴan Kishin Ƙasa

“Wurin da filin jirgin saman farar hula da na sojoji duk a haɗe yake, don haka ba a tabbatar ko sojoji ko fararen hula aka kai wa harin kai tsaye ba,” in ji Hiba Morgan.

Har yanzu dai babu tabbaci ko RSF na ƙoƙarin kai hari ne kan wani jirgin yaƙi da aka nuna a wani bikin nuna ƙarfin soji da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

Wannan hari ya ƙara jefa birnin Port Sudan cikin fargaba, inda aka dade ana ɗaukarsa a matsayin mafaka daga rikicin da ke addabar wasu sassan ƙasar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Sudan ke ci gaba da fuskantar mummunan rikici tsakanin dakarun gwamnati da RSF tun daga watan Afrilun bara.

Comments (0)
Add Comment