Robert Prevost, Ɗan Amurka Na Farko Ya Zama Sabon Fafaroma

Cardinal Robert Prevost daga ƙasar Amurka shi ne sabon Fafaroma da shugaban cocin Katolika na duniya bayan da aka zaɓe shi a birnin Vatican a ranar Alhamis.

Babban Cardinal na cocin ya sanar da wannan babban lamari ga dubban jama’a a dandalin St Peter’s Square inda ya ce: “Sabon Fafaroman zai yi amfani da sunan Pope Leo na sha huɗu.”

Wannan zaɓen ya biyo bayan rasuwar tsohon Fafaroma Francis, kamar yadda jagororin cocin suka tabbatar, kuma an gudanar da shi cikin tsarin sirri da dokokin cocin suka tanada.

WANI LABARI: Ministan Tsaro Ya Ƙalubalanci Yin Taron Ƙasa Don Inganta Tsaro, Ya Yi Kiran Sauyin Dabaru

Cardinal Prevost, wanda ya fito daga jihar Chicago, ya shahara wajen ƙarfafa alaƙa tsakanin cocin da al’umma musamman a fannonin ilimi, jin ƙai, da ayyukan ceto.

Ana kallon wannan zaɓe a matsayin juyin-juya hali a tarihi, domin shi ne Fafaroma na farko daga Amurka da ya hau wannan kujera.

Masu sharhi na ganin cewa wannan na iya kawo sabbin tsare-tsare a cikin cocin, musamman dangane da matsalolin duniya da sabbin ƙalubalen addinai.

A halin yanzu, ɗaruruwan Katolikawa a duniya na murnar wannan sauyi tare da fatan sabon jagoran zai tafiyar da cocin cikin zaman lafiya da cigaba.

Comments (0)
Add Comment