Sabon Dan Majalissar Wakilai Ya Bayar Da Gudunmawar Shanu 59 Don Bikin Sallah A Mazabarsa

Sabon Dan Majalissar Wakilai mai jiran rantsuwa na Mazabar Gwamnatin Tarayya ta Maru/Bungudu a Jihar Zamfara, Abdulmalik Zubairu a jiya Talata, ya bayar da gudunmawar shanu 59 ga al’ummar mazabarsa domin gudanar da bikin karamar sallah.

Da yake jawabi a lokacin rarraba shanun a Bungudu, dan majalissar mai jiran rantsuwa ya ce, ya yi hakan ne a matsayin wani shirinsa na samar da walwala ga matanen mazabarsa a lokutan bukukuwan Sallah.

Abdulmalik, wanda ya samu wakilcin tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Bungudu, Basharu Bello-Auki ya ce, masu morar gudunmawar sun hada da shugabannin APC na mazabu 21 na kananan hukumomin Bungudu da Maru.

Sauran masu rabauta da tagomashin sun hada da marayu, zawarawa, ‘yan gudun hijira, matasa da kuma kungiyoyin mata.

“Wannan wani kari ne a kan kayan abinci wadanda aka rarraba a farkon watan Ramadan.

Dan Majalissar ya yi kira ga ‘yan kwamitin rabon da su tabbatar da adalci da gaskiya a rabon dabbobin.

Da yake magana a madadin wadanda suka more tagomashin, shugaban Zannah Foundation na yankin mazabar Maru, Nasiru Sani, ya yabawa dan majalissar mai jiran rantsuwa game da kyautatawar da yai musu.

Nasiru Sani ya kuma ce, kwamitin zai tabbatar da adalci wajen rabon dabbobin ga wadanda aka ware zasu mora.

NAN

Karamar SallahZamfara
Comments (0)
Add Comment