Dan Majalisar Wakilai Hon Ibrahim Usman Auyo daga mazaɓar Hadejia/Auyo/Kafin Hausa a Jihar Jigawa ya yi zafafan tuhume-tuhume cikin wani bidiyo da ya yaɗu inda ya bayyana cewa wasu ƴan majalisa na karɓar kuɗi kafin su ɗauki nauyin gabatar da Motions da Bills a majalissar.
Auyo ya ce maganganunsa ya fara ne a matsayin martani ga sukar da wasu ƴan mazaɓarsa suka yi masa game da yadda yake aiki a majalisa.
Ya zargi wasu ƴan majalisa da mayar da aikin gabatar da dokoki kasuwanci ta hanyar cewa aikin ya zama “contract jobs” ma’ana ana siyar da damar gabatarwa.
Wani abu daga cikin maganganun sa shi ne cewa “Kowanne gabatar da ƙudiri na cin tsakanin naira miliyan 2 zuwa miliyan 3 da miliyan 1” wanda ya ce haka ake biya kafin a karanta Bill a gaban Majalisar.
Hon Auyo ya ƙara bayanin cewa ko gabatar da ƙorafi ma ana buƙatar a biya kafin a ɗauki mataki sannan akwai buƙatar neman kamun ƙafa ga dukan ƴan majalisa 360 domin su goyi baya a ɗauki ƙudiri.
Duk da wannan zargi, Auyo ya musanta cewa shi kansa ya taɓa yin irin wannan aiki ga ƴan mazabarsa kuma ya ƙalubalanci waɗanda ke masa zargi da cewa “kowa ma waye zai iya fitowa ya ƙalubalance ni.”
Jaridar LEADERSHIP ta yi ƙoƙarin samun martani daga shugabancin Majalisar amma a lokacin haɗa wannan rahoto babu wata amsa daga gare su.
Idan har iƙirarin Auyo gaskiya ne, hakan zai nuna cewa akwai babbar matsala ta cin hanci a tsarin dokoki inda kuɗi ke rinjayar wanda zai yi magana a madadin al’umma.
Masu sa ido kan siyasa da sauran al’umma na neman a gudanar da cikakken bincike da matakan ladabtarwa don dawo da ƙarfin amincewa da Majalisa da kuma tabbatar da gaskiya a harkokin dokoki.