Sannanen Malamin Addinin Musulunci Sheikh Yusuf Ali Ya Rasu

Sannanen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yusuf Ali na Jihar Kano ya rasu yana da shekaru 73 a duniya.

Ɗansa, Muslihu Yusuf Ali ya sanar da rasuwar mahaifin nasa a wani rubutu da ya saki a manhajar Facebook a dare jiya Lahadi.

An haifi Sheikh Yusuf Ali a garin Gaya da ke Jihar Kano a shekarar 1950, ya fara aiki a sashin shari’a a shekarar 1974 inda yai ta samun ƙarin girma har ya kai matsayin Rijistara, Alƙali a Babbar Kotun Shari’a da kuma Darakta a Babbar Kotun Shari’a.

Ya yi ritaya daga aiki a shekarar 2009 tare da ci gaba da yin wa’azi da koyar da addinin Musulunci da samar da waraka ga al’umma.

An yi jana’izarsa a yau Litinin a gidansa da ke unguwar Tudun Maliki a Birnin Kano da misalin ƙarfe 1:30 na rana.

Sheikh Yusuf Ali
Comments (0)
Add Comment