Sauya Sunan Jami’ar Maiduguri Zuwa Muhammadu Buhari University Na Shan Suka

Sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa Muhammadu Buhari University da Shugaba Bola Tinubu ya sanar a makon jiya, na ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce a fadin Najeriya, musamman a jihar Borno da jami’ar take.

Wasu masana da ƴan ƙasar sun bayyana damuwa kan sahihancin matakin, inda suka ce babu wasu shawarwari da aka yi da Majalisar Dokoki kamar yadda doka ta tanada, yayin da wasu suka zargi gwamnati da rashin mutumta ra’ayin al’umma.

A cewar wani lauyan da yai hira a tashar Arise TV, Maxwell Opara, “An kafa jami’ar ne bisa doka ta musamman, amma shugaban ƙasa ya sauya sunanta ba tare da tuntuba ba, kuma hakan ba daidai ba ne a tsarin mulki da bin doka.”

WANI LABARIN: An Buƙaci Samar da Takardar Shaidar Kammala Karatun Almajirai Domin Ba Su Damar Ci Gaba da Karatu

A wani ɓangare kuwa, wata ƙungiya ta ƙaddamar da kokenta a yanar gizo tana neman shugaban ƙasa ya soke sauya sunan da yai, wanda a cikin sa’o’i ƙalilan ya samu sama da sa hannun mutane 7,500.

“Jami’ar Maiduguri ta fi zama alamar jajircewa da ci gaban ilimi a yankin Arewa maso Gabas fiye da komai, kuma canza sunanta na iya rushe gagarumar ma’ana da ta ƙunsa a zukatan jama’a,” in ji wani ɓangare na rubutaccen koken.

Comments (0)
Add Comment