Shekara Ɗaya Bayan Hukuncin Kotun Ƙoli, Gwamnatin Tarayya Ta Gaza Tabbatar Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi

Duk da hukuncin Kotun Koli a ranar 11 ga Yulin 2024 da ya bai wa ƙananan hukumomi ƴancin gudanar da kuɗaɗensu kai tsaye daga Asusun Tarayya, gwamnatin tarayya a ƙarƙashin Bola Tinubu ba ta tabbatar da wannan tsarin ba har kawo yanzu.

Kotun ta ce, “Tun da tsarin biyan (ƙananan hukumomi) ta jihohi bai yi aiki ba, a tsari na adalci ya kamata a biya kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye daga Asusun Tarayya.”

Amma bayan kafa kwamitin gwamnati mai mutane 10 a watan Agustan bara, an samu jinkiri da cikas, musamman daga jihohi da kuma matakan Babban Bakin Najeriya da suka buƙaci ƙananan hukumomin su kawo bayanan kuɗin shekaru biyu kafin buɗe asusun karɓar kuɗin kai tsaye.

Ƙungiyoyin ALGON da NULGE sun bayyana wannan jinkirin a matsayin wata dabara ta wuce gona da iri daga gwamnati da kuma gwamnoni don hana aiwatar da hukuncin kotun.

WANI LABARIN: Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya Ta Yi Allah-Wadai Da Sabon Tsarin Albashin Gwamnati

“Idan an hana ƙananan hukumomi su zaɓi bankin da suke so, to ba wani cikakken ƴanci ke nan aka ba su ba,” in ji Sakataren ALGON, Muhammed Abubakar.

NULGE ta ce rashin wannan ƴanci yana hana jama’a a matakin ƙananan hukumomi samun ayyuka kamar lafiya da ilimi da tsafta.

Lauyoyi da ƙungiyoyi irin su SERAP da CACOL sun zargi gwamnati da siyasantar da hukuncin da aka fitar, suna cewa gwamnati ba ta da shirin tabbatar da dokar.

Duk da haka, Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya ce a jiharsa ana aiwatar da ‘yancin ƙananan hukumomin da kaɗan da kaɗan, yana mai jaddada buƙatar duba tsarin biyan albashi da tabbatar da ingantacciyar kulawa a matakan ƙananan hukumomi a Najeriya.

Shugaban NULGE, Aliyu Haruna Kankara, ya ja hankalin gwamnati da cewa, “Idan aka ci gaba da jan ƙafa, jama’a za su ci gaba da shan wahala kuma muna iya fita zanga-zanga matuƙar ba a ɗauki mataki ba.”

Comments (0)
Add Comment