Shekarun Jigawa 32 Da Ƙalubalen Rashin Aikin Yi A Tsakanin Matasa

Daga: Ahmed Ilallah

Kwanci tashi asarar mai rai, inji masu iya magana,  a yau Jihar Jigawa ta ki shekaru 32 da kirkikra. Jahar da a ka yi ta domin raya karkara. A yanzu za a iya cewa san barka.

A shekarun nan na Jigawa 32, koba komai an samu gagarumin cigaba a fannoni daban daban, kama daga harkar ilimi, harkar lafiiya  dan bunkasa karkara, kusan a yanzu Jihar Jigawa na da ga cikin jahohi masu isassun hanyoyin mota davsuka hade muhimman garuruwa a jahar.

A yanzu jahar nada issasun makarantu da asibitoci, jaharma na kan gaba wajen samar  wa al’umar su.

Sai dai kash, a wannan karnin, babban kaluballen da ke addabar jahar shine karuwar talauchi a tsakanin al’umar jahar.

Daga cikin abin da ke kara wannan talauchi shine rashin aikin yi, mussaman tsakanin matasa.

Yawan mutanen Jigawa ya karu da sama da kashi hudu koma biyar, a yanzu a na maganar, al’ummar Jigawa sun kai kusan mutane miliyan bakwai.

KARANTA WANNAN: JANYE TALLAFI: Ya Kamata Gwamna Namadi Ya Motsa!

Yawan karuwar mutane ya hana tattalin arzikin wannan jaha, wannan ya haifar da karuwar rashin aikin yi a tsakanin matasa.

Kusan za a ce dukkanin aiyukan da su ka shafi karatun boko, kusan kashi saba’in gwamnatoci ne suke samar da shi, saboda karancin manyan kamfanoni ko masana’antu da su iya bawa matasan nan aikin yi.

Yanyin dangwamnatocin bata suka samu kansu da kuma yadda suka tafiyar da aiyukan su, wannan ya janyo rashin daukan aiki a guraben gwamnati wadatacce da zai bawa matasan nan abin yi.

Koda tsare-tsare na bayar da tallafi da samar da jari ga wannan matasa, shima ya kasa  yin inganci da zai ceto wannan matasa.

Rashin aikin yibga matasa ba karamin tasgaro  ya ke kawo ba wajen bunkasa tattalin arziki dama samar da tsaro.

Shin a wannan lokaci da saban gwamna Malam Umar Namadi ke jagoranta, kan iya kawo karshen wannan matsalar?

Gannin yadda gwamnatin a farkon hawanta ta kafa sabuwar  hukuma da zata kula da harkar matasa da samar da aiyuka, ko zata yi tasiri wajen samawa wannan matasa aiyuka yi.

Amma mu tuna a baya ma fa, gwamnatin da gabata  tayi kamanceceniyar wannan aikin, amma har yanzu matsalar aikin yi a tsakinin matasa  ba karamin kalubale bane.

alhajilallah@gmail.com

Jihar JigawaMatsalar Ma'aikata
Comments (0)
Add Comment