Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Faɗawa Gwamnoni Magana Kan Kuɗaɗen Da Suke Samu Daga Asusun Tarayya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnonin jihohi da su tabbatar da cewa kuɗaɗen da suka karɓa daga gwamnatin tarayya sun haifar da gagarumin ci gaba, musamman a matakin ƙananan hukumomi.

Ya bayyana hakan ne a yayin taron kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC na ƙasa, inda ya nuna damuwa da yadda ƴan Najeriya ke cigaba da bayyana rashin jin daɗi da tasirin gwamnatin da suka zaɓa.

Shugaba Tinubu ya ce, “Dole ne mu ƙara yin aiki tuƙuru. Jama’a har yanzu suna ƙorafi a ƙasa, ku gwamnonin jam’iyyar APC dole ne ku yayyafa ruwa a ƙasa.”

Ya ƙara da cewa, “Ba za mu yi watsi da jama’a ba; dole su ji sauyin gwamnati kai tsaye.”

WANI LABARIN: CIKAKKEN SHARHI KAN TATTALIN ARZIƘI: Alƙaluma Masu Kyau Amma Ƴan Najeriya Na Cikin Ƙunci

A cewar alƙaluman kuɗaɗen da aka tara daga haraji, gwamnatin tarayya ta samu naira tiriliyan 14.27 daga watan Janairu zuwa Yuni na shekarar 2025, abin da ke nuni da ƙaruwa da kaso 43 daga abin da aka tara a farkon rabin shekarar 2024.

A tsawon watanni 12 da suka gabata, Hukumar Rabon Kuɗi (FAAC) ta raba naira tiriliyan 11.195 ga jihohi da ƙananan hukumomi – inda jihohi suka karɓi tiriliyan 6.492, ƙananan hukumomi suka samu tiriliyan 4.704, yayin da gwamnatin tarayya ta samu tiriliyan 16.034 cikin tiriliyan 27 da aka tara.

Shugaba Tinubu ya ce babu ƙwaƙƙwarar hujja da zata gamsar da talaka sai an canja ƙalubale zuwa aikin gani da ido a ko’ina.

Ya jaddada cewa lokaci ya yi da za a tabbatar demokaraɗiyya ta fito fili a zahiri, ba a kan takarda ba.

Comments (0)
Add Comment