Shugaban Kasa mai Jiran Gado a Najeriya na Jam’iyyar APC, ya hana mataimakansa da masu kai masa ziyara amfani da wayoyin da ba a amince da su ba a Kasar France don gudun kar a tona asirin karfin jinyar da yake ciki in ji SaharaRepoters.
Tinubun dai ya fada rashin lafiya ne bayan tsattsauran yakin neman zaben da ya kai ga zama Shugaban Kasa mai Jiran Gado da kuma aikin neman zaben gwamnan Jihar Lagos da aka yi ranar 18 ga watan March.
A dai karshen watan March ne, wata majiya ta sanar da SaharaReporters cewa, har kawo wannan lokaci, likitoci na ci gaba da kulawa da Tinubu a wani asibiti da ya Paris na kasar France.
A ranar Talata, SaharaReporters ta gano cewa, tsohon gwamnan Jihar Lagos din wanda ya cika shekara 71 ‘yan kwanakin da suka gabata a lokacin ba ya Najeriyar, ya hana mataimakansa da sauran mutane da ke zuwa kusa da shi amfani da wayoyin da bai amince da su ba, don kare yada yanayin lafiyarsa.
Wata majiya daga kusa da shi ta ce, “Tinubu ya hana ma’aikatansa da masu kula da shi amfani da wayoyin hannunsu wadanda bai amince da su ba, saboda tsoron kar a bayyana girman jinyar da yake a France.
“Yana tsoron cewa, akwai wani da ke kusa da shi da yake tona asirin abubuwa ga ‘yanjarida a daidai lokacin da ranar 29 ga May take kara kuratowa lokacin da za a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa, mutanensa na kokarin hana bayyanar bayanai game da lafiyarsa.”
A watan February ma, SaharaReporters ta rawaito cewa, wani faifan bidiyo ya zagaya a kafafen sadarwa na zamani wanda yake nuna Tinubu da wata jika da ake zargin ta fitsari ce a daidai mazaunansa lokacin da ya kaiwa Awujale na Ijebuland ziyara.