Soja Na Samun Ƙasa Da Naira 50,000 A Wata – In Ji Babban Hafsan Sojojin Najeriya

Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Janaral Christopher Musa ya bayyana cewar ana biyan sojojin Najeriya albashin naira 50,000 ne a kowanne wata, yayin da shi kansa da sauran sojoji ke samun naira 1,200 a matsayin alawuns na aiki a kowacce rana.

Janaral Musa ya bayyana hakan ne a tattaunawar da yai kan halin da walwalar sojoji ke ciki da gidan talabijin na Channels a jiya Talata.

Ya ce, alawuns na aiki da yake samu wanda suke amfani da shi domin cin abinci lokacin aikin, shi a matsayinsa na Janaral ana ba shi naira 1,200 ne kacal haka sauran manyan sojoji da ƙanana.

Ya ce sojojin Najeriya na karɓar albashin da ya gaza naira 50,000, inda ya bayyana cewa, fatansa shine sojojin su samu albashin da ya dace da aiyukan da suke yi domin ƙara musu ƙarfin guiwa.

Ya kuma bayyana cewar akwai buƙatar ƙara yawan barikin sojoji a Najeriya duk da dai sojoji 15,000 aka ɗauka a ƴan shekarun da suka gabata.

Ya ƙara da cewa, duk aiyukan sojoji shine kare ƙasa daga matsalolin da zasu zuwa mata daga ƙetare, dole ta sa suna aiki a cikin gida, saboda bai kamata su ƙyale cikin ƙasa ba idan ya kamata da wuta.

Christopher MusaSojojin Najeriya
Comments (0)
Add Comment