Sojoji Sun Farmaki Ofishin KAEDCO Da Ke Kebbi, Sun Ci Zarafin Ma’aikata Saboda Rashin Wutar Lantarki

Sojoji dauke da makamai sun kai farmaki ofishin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna KAEDCO a jihar Kebbi tare da cin zarafin ma’aikatan da suka kasa samar musu da wutar lantarki a barikinsu.

Manajan kamfanin na jihar Kebbi, Gaddafi Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani faifan bidiyo da aka yada ta yanar gizo, inda ya ce sojojin sun lakadawa ma’aikata da kwastomomi duka a ranar Asabar din nan.

Ya ce sojojin sun zargi KAEDCO da rashin samar da isasshiyar wutar lantarki a barikin duk da sadaukarwar da suke yi wa kasa.

Ya ce mutane 14 da suka hada da jami’an tsaro masu zaman kansu, kwastomomi, da ‘yan kasuwa an yi musu dukan tsiya ba tare da tausayawa ba, tare da tilasta musu yin tsallen-kwado.

“Da misalin karfe 1 na rana, jami’an sojoji suka mamaye ofishinmu. Ina zaune tare da shugabana wanda ya zo daga Sokoto. Da muka fito waje, sai muka ga suna cin zarafin wasu ma’aikatanmu da abokan cinikinmu.

“An umarce su da su cire tufafinsu su yi tsallen kwadi.

“Lokacin da muka tuntube su, sai suka ce mana sun zo ne domin yin korafin cewa ba a ba su isasshiyar wutar lantarki ba. Sun kuma ce rashin mutunci ne mu mu sami wuta mu bar su su cikin duhu.

“Na shaida musu cewa a cikin watanni shida da aka dawo da ni nan, ban taba samun korafi daga barikin ba, amma suka sha alwashin ba zasu bari masu yin tsallen kwadi su tsaya ba har sai an dawo musu da wuta a cikin bariki. Sai na ba da umarnin a dawo musu da wutar nan take,” in ji shi.

Wata sanarwa da mataimakin babban sakataren Kungiyar Manyan Ma’aikatan Wutar Lantarki da Kamfanonin Hadin Gwuiwa, SSAEC mai kula da yankin Arewa, Haruna Tinau, ya fitar, ta yi Allah-wadai da harin da sojojin suka kai wa mambobinsu tare da neman a dakatar da barikin Birnin Kebbi daga samun wuta gaba daya har sai an kamo masu laifin.

Wutar Lantarki
Comments (0)
Add Comment