Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 152, Sun Kama 109, Sun Ceto Mutane 91

Sojoji sun kashe ƴan ta’adda 152, sun kama 109, sun ceto mutane 91 da aka yi garkuwa da su, a yayin da suke yaƙi da matsalar tsaro a fadin kasar nan cikin makon da ya gabata.

Sojojin sun kai hari kan sansanonin wasu manyan shugabannin ƴan ta’adda a Ƙaramar Hukumar Safana ta Jihar Katsina da Ƙaramar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna, inda suka ruguje maɓoyarsu.

Haka kuma, sojojin sun kama wasu mata biyu da ke hada baki da ƴan ta’adda wajen yin sulhu da dangin waɗanda aka sace domin neman kudin fansa.

A yankin Niger Delta, sojojin sun gano wuraren tace mai ba bisa ƙa’ida ba guda 58, kuma sun daƙile yunƙurin satar man fetur na kimanin naira miliyan 795.

Bugu da kari, sun hana satar lita 725,920 na ɗanyen mai da lita 475,250 na man da aka tace ba bisa ka’ida ba a jihohin Rivers da suka hada da yankin Bugama, Idama, da Krakrama.

Kakakin rundunar sojoji, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana cewa, sun kuma kwace makamai 183 da harsasai 4,443 daga hannun ƴan ta’adda a wurare daban-daban.

A cikin makon da ya gabata, sojojin sun kashe ƴan ta’adda 31, sun kama mutane 7, sun ceto mutane 26, tare da kwace makamai da dama a jihohin Borno, Yobe, Kaduna, da sauran sassan ƙasa.

Comments (0)
Add Comment