Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 96, Sun Kama Wani Babban Kwamanda A Arewa

Hedikwatar Tsaro ta sanar da cewa dakarun sojin Najeriya sun kashe aƙalla ƴan ta’adda 96 kuma sun kama mutum 227 da ake zargi da ta’addanci, ciki har da wani kwamandan ƴan ta’adda da ake nema ruwa a jallo, yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan soji a yankin Arewa.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a, Manjo Janar Buba Edward, Daraktan Harkokin Watsa Labarai na Hukumar Tsaro, ya bayyana cewa cikin waɗanda aka kama har da Usman Maisaje, wani babban kwamandan ƴan ta’addar.

An bayyana cewa Maisaje aboki ne na kusa ga Kachalla Boka, wani shahararren shugaban ƴan ta’adda da har yanzu rundunar sojin ke neman sa.

Janar Buba ya jaddada muhimmancin kama Maisaje, inda ya bayyana cewa kwamandan da aka kama yana ba da haɗin kai ga sojoji, kuma yana ba su bayanai masu amfani, wadanda ke taimakawa wajen gudanar da ƙarin ayyukan soja.

“A cikin makon da ya gabata, dakaru sun kashe ƴan ta’adda 96, sun kama mutum 227, kuma sun ceto mutum 157 da aka yi garkuwa da su,” in ji Buba.

“Dakarun a fagen daga na NC sun kama wani shahararren kwamandan ƴan ta’adda mai suna Usman Maisaje. Kwamandan da aka kama, aboki ne na kusa da wani fitaccen shugaban ƴan ta’adda mai suna Kachalla Boka.

“Kamen ya kasance mai muhimmanci wajen tattara bayanan sirri, domin (wanda aka kama) yana ba da haɗin kai tare da samar wa sojoji bayanan da suke buƙata don cigaba da ayyukansu.”

Wannan ci gaban na baya-bayan nan yana cikin wani yunƙuri na ci gaba da murƙushe ayyukan ƴan ta’adda a yankin Arewa.

Rundunar sojin na ci gaba da ƙarfafa ayyukanta don tarwatsa sansanonin ƴan ta’adda, tana mai mayar da hankali kan manyan shugabanni da abokan aikinsu.

A baya-bayan nan dai, sojojin sun bayyana nasarori da dama, ciki har da kashe manyan ƴan ta’adda da kuma rushe sansanoninsu.

Nasarori A Yankin Kudu-Maso-Kudu

A wani cigaba mai alaka da wannan, dakarun soji da ke aiki a yankin Kudu-Maso-Kudu sun samu nasarori masu yawa a yaƙin da suke da satar man fetur.

Manjo Janar Buba ya bayyana cewa dakarun sojin sun ƙwato man fetur da aka sace wanda darajarsa ta kai Naira miliyan 712 kuma sun kama mutane 45 da ake zargin barayin mai ne.

“Dakarun a yankin Niger Delta sun gano tare da lalata ramuka hudu da ake amfani da su wajen sata, kwale-kwale 48, ganguna 52 da kuma tankokin ajiya 38,” in ji shi.

“Sauran kayayyakin da aka gano sun hada da manyan tukunyar girki guda 55, jiragen ruwa masu sauri guda biyu, babur mai kafa uku guda uku, wayoyin hannu guda shida, motoci guda shida, da kuma gano haramtattun wuraren tace mai guda 60. Dakarun sun karɓo lita 712,535 na man fetur da aka sace da kuma lita 76,800 na dizal da aka tace ba bisa ƙa’ida ba.”

Rundunar sojin ta kuma ƙwato makamai manya 71 da kuma manyan kayan yaƙi da suka haɗa da harsasai guda 1,463.

Wannan yaƙi da masu satar mai wani ɓangare ne na wani shiri na rage ayyukan haramtattun hada-hadar man fetur a yankin Niger Delta, wanda ke ci gaba da yin illa ga tattalin arzikin man fetur da kuɗaɗen shiga na Najeriya.

Wadannan nasarori na baya-bayan nan sun nuna ƙudirin rundunar sojin na ci gaba da yaƙi da ta’addanci a Arewa da kuma ayyukan satar ɗanyen mai a yankin Kudu, don tabbatar da tsaron kasa baki ɗaya.

Matsalar Tsaro
Comments (0)
Add Comment