Sule Lamido Zai Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwarsa

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya shirya ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa da ya rubuta mai taken Being True to Myself (Faɗawa Kaina Gaskiya) a ranar Talata, 13 ga watan Mayu, a birnin tarayya Abuja, lamarin da ke janyo hankalin masu bibiyar tarihin siyasar Najeriya.

Shugaban kwamitin shirya bikin ƙaddamarwar, Sanata Mustapha Khabeeb, ya bayyana a wani taron manema labarai cewa wannan littafi “zai buɗe sabuwar hanya wajen fahimtar haƙiƙanin tarihin siyasar Najeriya daga ƙarshen mulkin farar hula na biyu, zuwa mulkin soja har zuwan jamhuriya ta huɗu.”

A cewarsa, littafin na ɗauke da bayanai masu zurfi da ke bayyana rikice-rikicen siyasa, cin amana da yaƙin neman iko da suka kasance jigon tarihin dimokaraɗiyyar Najeriya.

“Ba wai labarin rayuwar mutum ɗaya ba ne kaɗai, amma wani kundin tarihi ne da ke bayyana halin da shugabanci da dimokaraɗiyya suka kasance a Najeriya,” in ji shi.

WANI LABARIN: Za A Gyara Tsarin NYSC A Najeriya, Yayin Da Gwamnati Ta Kafa Kwamiti Don Yin Hakan

Ya bayyana cewa littafin ya tattauna kan yadda Lamido ya samo asali daga ɗan gwagwarmaya zuwa babban ɗan siyasa, minista da dattijo a harkokin siyasa, inda aka fi mayar da hankali kan rawar da ya taka a matsayinsa na Ministan Harkokin Waje a ƙarƙashin mulkin Shugaba Obasanjo da kuma matsayinsa a turka-turkar June 12 da kafa jam’iyyar PDP.

“Shugaba Olusegun Obasanjo wanda ya rubuta gabatarwar littafin, ana sa ran zai halarci bikin ƙaddamarwar a matsayin Babban Baƙo na Musamman.”

Sanata Khabeeb ya kuma nuna cewa Sule Lamido ya ci gaba da tsayawa kan aƙidunsa duk da cikas da ƙalubalen siyasa da ya fuskanta, ciki har da shari’a da aka shafe shekaru bakwai ana yi a kansa da ƴaƴansa kan tuhume-tuhume da kotu ta ƙarshe ta wanke su daga baya.

“Wannan wani labari ne da ya cancanci a faɗa,” in ji Sanata Mustapha Khabeeb.

Comments (0)
Add Comment