Sunday Igboho Ya Jaddada Yunƙurinsu Na Kafa Ƙasar Yarabawa A Sakonsa Na Sabuwar Shekara

Cif Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya aike da sakon gaisuwar Sabuwar Shekara ga al’ummar Yarabawa a faɗin duniya, yana mai jaddada cikakken ƙudurinsa kan fafutukar samun cin gashin kai ga al’ummar Yarabawa. 

A wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Olayomi Koiki, Igboho ya yi addu’ar samun wadata a Sabuwar Shekara tare da tabbatar da cewa fafutukar kafa Ƙasar Yarabawa mai cin gashin kanta ba za ta gushe ba.

“Kalmar da muka runguma ita ce, ‘Ba bu ja da baya.’ Wannan shi ne lokaci na samun haɗin kai, jarumta da mayar da hankali. Mun ƙuduri aniyar cimma burinmu, kuma muna kira ga duk Yarabawa da su shirya wa abin da ke tafe,” in ji Igboho.

Ya kuma yi kira ga gudanar da zanga-zanga cikin lumana don tallafa wa wannan fafutuka, yana mai cewa, “Za mu ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana don tabbatar da haƙƙoƙinmu na samun ƴancin kai. Kada ku ji tsoro – wannan fafutukar za ta kawo canjin da muke fata.” 

Igboho ya yi kira ga samun haɗin kai da ɗaukar matakai masu kyau tsakanin al’ummar Yarabawa, yana mai cewa, “Hanyarmu za ta iya kasancewa mai wahala, amma abin da muke nufi ya bayyana, kuma nasarar mu tabbas ce.” 

A cikin saƙonsa, ya tabbatar wa Yarabawa cewa burinsu zai zama gaskiya nan ba da jimawa ba, yana mai cewa, “Allah ya sa wannan Sabuwar Shekara ta kawo farin ciki, zaman lafiya, da cikar buri ga duk Yarabawa a faɗin duniya. Yayin da muke shiga wannan sabon yanayi, muna ƙara kusantar cimma burinmu fiye da da.”

Comments (0)
Add Comment