TAKARDUN TINUBU: Shaidar Kammala Karatun Da Tinubu Ya Miƙa Wa INEC Ta Bogi Ce, Inji Rijistaran Jami’ar Chicago

Rijistaran Jami’ar Jihar Chicago, Caleb Wesberg ya bayar da shaida ƙarƙashin rantsuwa inda ya ce, takardar shaidar kammala karatu wadda Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya miƙawa Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ba takarda ce da jami’ar ta bayar ba.

Rijistaran da ya bayar da shaida a jiya Talata kan shari’ar da ake, biyo bayan hukuncin Alƙaliya Nancy Maldonado a ranar Litinin a kan buƙatar Jami’ar Chicago ta fitar da bayanan karatun da Bola Tinubu yai a cikinta, ya ce, tambari (logo) na makaranta a jikin takardun da Tinubu ya gabatar, makarantar ba ta san da shi ba.

Rijistaran ya kuma ce, Bola Tinubu ya nemi shiga jami’ar a matsayin namiji, kuma jami’ar ta bai wa namiji ne damar shiga jami’ar ba mace ba, sai dai kuma bai san me yasa takardun Tinubu na makarantar SouthWest suke ɗauke da jinsin mace ba.

KARIN LABARI: Tinubu Ya Sha Ƙasa A Kotun Amurka, Yayin Da Kotun Ta Umarci Jami’ar Chicago Ta Bayyana Wa Atiku Bayanan Karatunsa

An dai ta karɓar bayanai kan takardun Tinubu a kotun har na tsawon awanni 5, inda aka ƙare da misalin ƙarfe 9:30 na dare a agogon Najeriya.

A yanzu dai kotun zata gabatar tare da tabbatar da miƙawa lauyoyin Atiku Abubakar cikakkun bayanan da suka nema domin yin amfani da su a shari’ar da ake kan cancantar tsayawar Bola Tinubu takarar shugaban ƙasa.

Idan za a iya tunawa dai, ɗaya daga cikin hujjojin Atiku Abubakar na cewar Bola Ahmed Tinubu bai cancanci zama shugaban Najeriya ba, akwai zargin cewar Tinubu bai gabatar da shaidar yin karatu ta haƙiƙa ga INEC ba wanda hakan ke nuni da cewar ya yi amfani da takardun bogi.

Atiku AbubakarBola Ahmed TinubuJami'ar Jihar Chicago
Comments (0)
Add Comment