Talauci A Najeriya Zai Zarce Hasashen Bankin Duniya Kwanan Nan Saboda Tsadar Man Fetur

Masana tattalin arziƙi sun yi gargaɗin cewa adadin ƴan Najeriya da ke ƙasa da layin talauci na iya zarce hasashen Bankin Duniya na mutane miliyan 104, sakamakon hauhawar farashin fetur da matsalolin samar da abinci da ƙasar ke fuskanta.

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan masu fama da talauci a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 46 cikin 100 a shekarar 2023, wanda ke nuni da mutane miliyan 104 ne da ke fama da ƙangin talauci a ƙasar.

A cikin rahoton da bankin ya fitar an nuna yadda adadin masu fama da talauci ya tashi daga kashi 40 cikin 100 a shekarar 2018 zuwa kashi 46 cikin 100 a shekarar 2023, yayin da adadin talakawa ya ƙaru daga miliyan 79 zuwa miliyan 104.

Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki da ƙarancin ci gaban tattalin arziki ya jefa karin mutane miliyan 24 cikin talauci, inda adadin talakawa a birane ya ƙaru daga miliyan 13 zuwa miliyan 20, yayin da a karkara ya ƙaru daga miliyan 67 zuwa miliyan 84.

Duk da cewa Bankin Duniyar ya yi hasashen cewa sauye-sauyen tattalin arziƙin Shugaba Bola Tinubu daga shekarar 2024 zuwa 2026 za su rage ƙaruwar talauci, wasu masana sun bayyana cewa ƙarin farashin fetur da wasu manufofi na gwamnati za su sa yawan talakawan ya zarce wannan hasashe saboda tsadar kayayyaki da rashin ƙaruwar albashi.

Farfesa Taiwo Owoeye daga Jami’ar Jihar Ekiti ya ce ƙarin farashin fetur da ya kawo hauhawar kuɗin sufuri da kayayyakin masarufi zai ƙara matsin lamba kan talakawa da tattalin arzikin kasa.

Shi ma wani masanin tattalin arzikin harkokin noma, Tobi Awolope, ya ce hauhawar farashin fetur zai ƙara tsananta matsalar talauci da damuwar da talakawa ke fama da ita a ɓangaren ƙarancin abinci.

Comments (0)
Add Comment