Tallafin Naira Miliyan 20 Ga Nakasassu Na Sanata Malam Madori Gagarumin Aikin Alheri Ne

Daga: Ahmed Ilallah

Tabbas a wannan bigere da a ke na jarrabawar matsanancin yanayin na tattalin arziki dà ma duniya take ciki, duk mai tausayi yayi nazarin yaya Yan uwanmu suke cki, wayanda Allah yayi wa jarrabawar nakasa.

A irin wannan lokacin da kusan kowa yana cikin yanayin kuncin rayuwa, a fadin Nigeria, wannan yanayin mutane masu lafya ma kuka suke yi sanadiyyar matsin tattalin arziki, Yaya kuma Yan uwanmu nakasassu suke fama?

Duk Bawan Allahn da yake da tunanin kawo tsarin da zai kalli wannan bayin Allahn da yanayin da suke cike, wajen kawo mu su tsarin da zai tallafawa rayuwar su, tabbas wannan shugabane mai fikira da kuma dogon hangen nesa.

A nazari da a kayi na irin tallafi da masu mukami da akasari a ke rabawa al’ummah, kusan a kan manta da yan uwa masu bukata ta mussamman, a yanayin da ba a manta da su ba, kulawar da a ke basu kalilan ce, A wasu lokutan in anzo irin wannan bada tallafi a kan basu kason da bai wuce goma sha a cikin dari, koma abun  da ya gaza haka.

Wannan ita ce kulawa da a ka taba wa irin wadannan mutane a tarihince a wannan yankin na Jigawa ta Gabas, kai a ma fadin Jihar Jigawa, a ce yau wani mai mulkî yayi nazarin halin da wannan mutane suke çiki, har yayi musu tanadi da kulawar tasu ta mussamman.

Fatan mu shine wannan sanätan ya dore da irin wannan aiyuka da ya somo na alkhairi da kuma fadada shi zuwa kowane bangare na al’ummah.

Ahmed Ilallah ya rubuto daga Hadejia

Ahmed IlallahSanata Malam Madori
Comments (0)
Add Comment