Waɗanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke son naɗawa ministoci su 14 ne cikin 28 suka je Majalissar Dattawa a yau domin a tantance su.
A makon da ya gabata ne ranar Alhamis, Shugaban Majalissar Dattawa Godswill Akpabio ya bayyana sunayen mutane 28 da Shugaban Ƙasa ke son naɗawa ministoci.
Waɗanda suka je Majalissar Dattawan a yau sune:
- David Umahi (Ebonyi);
- Adebayo Olawale Edun (Ogun);
- Nasir El-rufai CON (Kaduna);
- Ahmed Musa Dangiwa (Katsina)
- Chief Uche Geoffrey Nnaji (Enugu);
- Stella Okotete (Delta);
- Dele Alake (Ekiti);
- Adebayo Adelabu (Oyo);
- Muhammad Idris (Niger);
- Professor Ali Pate (Bauchi);
- Doris Anite Uzoka (Imo);
- Lateef Fagbemi SAN (Kwara);
- Hon. Ekperikpe Ekpo (Akwa Ibom);
- Barr Hannatu Musawa (Katsina).