Najeriya ta miƙa buƙatar samun gurbi a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a taron majalissar karo na 79 da ake gabatarwa a birnin New York.
Najeriyar ta ce ta taka muhimmiyar rawa a ayyukan kiyaye zaman lafiya tare da tura fiye da sojojinta fiye da 200,000 zuwa ayyukan Majalisar Dinkin Duniya a gurare daban-daban.
Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya ce Najeriya ta cancanci samun gurbi a kwamitin saboda rawar da ta taka.
Badaru ya yi wannan jawabi ne a taron Tattaunawa don Gaba, ‘Summit of the Future’ da aka gudanar a birnin New York, na Amurka.
Shi dai Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na da mambobi 15 da ke da alhakin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya.
Har ila yau, kwamitin yana da ikon kafa rundunonin kiyaye zaman lafiya da sanya takunkumi da amincewa da ayyukan soji.
Badaru ya ƙara da cewa tun daga shekarar 1960 Najeriya ta yi aiki a Congo wajen tabbatar da zaman lafiya, sannan kuma ta halarci ayyukan kiyaye zaman lafiya a kasashe daban-daban kamar Côte d’Ivoire, Liberia, da kuma Sudan.
Ya ce Najeriya ta bayar da gudunmawa sosai a bangarorin kuɗi, kayan aiki, da jami’an tsaro na farar hula abun da ya sa ya kamata a gyara tsarin Kwamitin Tsaro domin bai wa Afirka gurbi na din-din-din.
Ministan ya ce akwai buƙatar gina rundunonin soji masu karfi a Afirka domin yaƙar ta’addanci.
Ya kuma jaddada muhimmancin kafa rundunar musamman mai taken ‘African Standby Force’ tare da samar da kayan aiki da goyon baya ga Afirka.
Har ila yau, Badaru ya yi kira ga ƙasashen duniya da su ƙarfafa matakan daƙile safarar makamai da manyan bindigogi inda ya ce, lokaci ya yi da za a ɗauki matakin gaggawa kan hakan.
Ministan ya jaddada bukatar daukar matakan tsaro na kasa da kasa domin yakar ta’addanci da samar da zaman lafiya a duniya.