Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Inganta Gwamnati Da Ci Gaban Tattalin Arziƙi A Jigawa Ya Fito Da Muhimman Batutuwa

A wani yunƙuri na inganta walwalar al’umma da kyautata harkokin mulki, an gudanar da taron kwanaki biyu a Kano tsakanin wakilan Jiha da na ƙungiyoyin farar hula domin gano matsalolin dake hana samun ingantaccen ci gaba a Jigawa, musamman a fannoni huɗu: mulki, tattalin arziƙi, sauyin yanayi, da walwala da tsaro na zamantakewa.

Taron, wanda aka shirya a ƙarƙashin shirin PACE (Partnership for Agile Governance & Climate Engagement) da goyon bayan FCDO da haɗin gwiwar Ma’aikatar Tsare-tsare da Tattalin Arziki ta Jihar Jigawa, ya kasance matakin farko na ƙirƙirar haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin gwamnati da al’umma.

Ɗaya daga cikin burin taron shi ne samar da hanyar tattaunawa tsakanin gwamnati da wakilan al’umma domin warware matsalolin da suka shafi sauyin yanayi da ingancin mulki.

An bayyana cewa taron zai taimaka wajen samar da dabarun warware matsalolin da suka dabaibaye jihar tare da tallafawa gwamnati wajen yanke shawarar da za ta amfani jama’a.

KARANTA WANNAN MA: NOA Ta Yabawa Davido Bisa Tallata Najeriya a Duniya, Ta Ce Ya Zama Wakilin Ƙasa Na Gari

“Mun ga yadda jama’a da gwamnati suka zauna a tebur guda domin nazari da fidda mafita, lamarin da ke nuna ci gaba mai kyau,” in ji daya daga cikin mahalarta.

Manyan jami’an gwamnati da suka halarci taron sun haɗa da Akanta Janar na Jigawa, manyan sakatarorin gwamnati daga ma’aikatun tsare-tsare da na muhalli, da kuma wakilan kungiyoyin farar hula da suka shafi ci gaban tattalin arziƙi da gwamnati.

An gudanar da taron ne a Tahir Guest Palace da ke birnin Kano inda aka samu zaman tattaunawa da musayar ra’ayoyi da suka janyo hankalin kowane ɓangare.

Shirin PACE ya bayyana aniyar cigaba da aiki tare da gwamnati domin aiwatar da abubuwan da aka cimma a wannan taro.

Taron ya nuna buƙatar ƙarfafa dangantaka tsakanin gwamnati da al’umma domin tabbatar da ingantaccen mulki da cigaban al’umma a Jihar Jigawa.

Comments (0)
Add Comment