TATTALIN ARZIƘI: Ajiyar Kuɗin Waje ‘Foreign Reserve’ Na Najeriya Ya Kai Dala Biliyan 41 – Fadar Shugaban Ƙasa

Bayo Onanuga, mai ba wa shugaban ƙasa shawara a fannin yaɗa labarai da tsare-tsare, ya bayyana cewa ajiyar kuɗin waje na Najeriya ya kai dala biliyan 41 a ranar 19 ga Agusta.

Bisa bayanan CBN, ajiyar kuɗin waje ta kai $41,001,830,139.96 yayin da net foreign reserve ya kusan kai wa dala biliyan 40.3.

Onanuga ya ce wannan ya faru ne ba tare da manyan kuɗaɗen shiga daga man fetur ba saboda farashin mai na raguwa.

A cewarsa, “duk wannan kulawa ce ta tattalin arziƙi ta Shugaba Bola Tinubu” wadda ta taimaka wajen ƙara yawan kuɗin ajiyar ƙasa.

Ya yi kakkausar suka ga ƴan adawa yana mai cewa ba za su yarda da nasarar ba saboda tsananin son samun mulki.

Masu sharhi sun ce wannan matakin zai iya ƙarfafa kasuwanci da ƙwarin gwiwa a ƙasar nan.

Sai dai wasu masana tattalin arziƙi sun gargaɗi cewa haƙƙin tabbatar da ɗorewa da raguwa a hauhawar farashi sun rage a hannun gwamnati.

Comments (0)
Add Comment