Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana ganawa da Babbar Daraktar Hukumar Kasuwanci ta Duniya, WTO, Farfesa Ngozi Okonjo Iweala a Fadar Shugaban Ƙasa, Villa da ke Abuja.
Farfesa Okonjo Iweala dai ta iso Fadar Shugaban Ƙasa ne da misalin ƙarfe 2 da mintuna 50 na rana, tare da tsohon Ƙaramin Ministan Lafiya a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan, Dr. Ali Pate.
Ita dai Farfesa Okonjo Iweala tsohuwar Ministar Kuɗi ce kuma Ministar da ta kula da Tattalin Arziƙi a lokacin gwamnatin Jonathan.
Ana tsammanin abubuwan da zasu tattauna zasu kasance kan dabarun farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya.