Tinubu Ya Lalata Tattalin Arzikin Najeriya Fiye Da Yanda Buhari Ya Lalata Shi – Hakeem Baba-Ahmed

Tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara a ofishin mataimakin shugaban ƙasa kan al’amuran siyasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya caccaki gwamnatin Tinubu, yana mai cewa tattalin arziƙin Najeriya ya taɓarɓare fiye da yadda Muhammadu Buhari ya bar shi.

A cikin wata hira da aka watsa a Channels TV, ya ce: “Ya ƙara ɓaci sama da yanda Buhari ya bar shi,” yana mai kare ra’ayinsa na rubuta buɗaɗɗiyar wasiƙa ga shugaba Tinubu yana buƙatar kada ya sake tsayawa takara a 2027.

Ya bayyana cewa ko da yake gwamnatin Tinubu ta zo da tsare-tsaren gyara kamar cire tallafin fetur da sakin Naira ta nemawa kanta daraja, hakan ya ƙara hauhawar farashin kaya daga 22.41% zuwa 34.6%.

KARANTA WANNAN: EFCC Ta Fara Bincike Kan Tsoffin Shugabannin NNPC Kan Badaƙalar Dubunnan Biliyoyi

Ya ƙalubalanci alƙaluman da gwamnati ke bayarwa, yana cewa, “Wannan kawai wata ƙididdiga ce da gwamnati ke yawan maimatawa . . . anya kuwa shugabanninmu sun san yanda mutane suke rayuwa?”

Baba-Ahmed ya ƙara da cewa, “Ana zubar da jinin mutane a yanzu sama da yanke a shekaru biyu na baya,” yana mai kokawa kan taɓarɓarewar tsaro da talauci da ake ciki.

Ya ce ya yanke shawarar barin muƙaminsa saboda rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da mulki, inda ya ƙara da cewa: “Mai Girma Shugaban Ƙasa, don Allah ka ƙara tsayawa takara”.

A ƙarshe, ya shawarci Tinubu da ya nemi matashi, mai lafiya da ƙwazo daga cikin jam’iyyarsa domin shugabancin ƙasar a gaba.

Comments (0)
Add Comment