Tinubu Ya Magance Zarge-Zargen Samun Rashin Jituwa Kan Ƴancin Ƙananan Hukumomi

Shugaba Bola Tinubu ya ƙaryata raɗe-raɗin cewa akwai rashin jituwa tsakaninsa da gwamnonin jihohi kan batun ƴancin ƙananan hukumomi, yana mai yin kira ga samun haɗin kai don bunƙasa cigaban ƙasa.

“An ce wai muna da rashin jituwa kan ƴancin ƙananan hukumomi. A’a… Babu wanda ke son karɓe su daga gare ku, amma muna buƙatar haɗin kai,” in ji Tinubu yayin wani taro na Sabuwar Shekara da gwamnonin jihohi a gidansa da ke Legas. 

Tinubu ya jaddada muhimmancin gwamnonin jihohi wajen cigaban ƙasa, yana mai kiransu da su mayar da hankali kan harkokin noma da daidaita tattalin arziƙi. 

Haka kuma ya bayyana cewa inganta aikin ƙananan hukumomi yana da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalolin al’umma a matakin karkara. 

“Ku ne jigon samun arziƙi da cigaban Najeriya. Tare, za mu gina ƙasa da za mu yi alfahari da ita,” in ji Shugaban. 

Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman AbdulRazaq, ya yaba wa jagorancin Tinubu, yana cewa an samu ci gaba sosai a harkokin noma da ayyukan jihohi.

“Mun samu nasarar shawo kan hauhawar farashi tare da sake fasalin tattalin arziƙi don samun cigaba na dogon lokaci.”

Comments (0)
Add Comment